Main menu

Pages

AN CAFKE DCP ABBA KYARI BAYAN NEMANSA DA AKE RUWA JALLO

 

YANZU-YANZU: ’Yan Sanda Sun Cafke DCP Abba Kyari, Bayan Da NDLEA Ke Nemansa.


’Yan sa’o’i bayan Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta shelanta neman korarren dan sandan nan, DCP Abba Kyari, bisa safarar miyagun kwayoyi, ’yan sanda sun tabbatar da cafke shi.


Jaridar Punch dai ta rawaito cewa an cafke shin ne tare da wasu mutum hudu da ake zargi a ranar Litinin.


Yanzu haka Abba Kyari na fuskantar bincike bayan wani rahoto na Hukumar Bincike ta Amurka (FBI) ya zarge shi da hannu a zargin da ake yi wa wani dan damfara ta intanet, Hushpuppi.


NDLEA ta ayyana Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sandan a matsayin wanda take nema ruwa a jallo bisa zargin harkalla ta miyagun kwayoyi.


Kakakin Hukumar NDLEA, Mista Femi Babafemi ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da ya gudana ranar Litinin a Abuja.


Majiyar mai tushe daga Hukumar NDLEA ta ce bincike ya nuna cewa DCP Kyari daya daga cikin ’ya’yan wata babbar kungiya ta kasa-da-kasa da ke hada-hadar miyagun kwayoyi a fadin duniya.


A watan Yulin bara ne Rundunar ’yan sandan Najeriya ta dakatar da Abba Kyari daga aikin dan sanda sakamakon zargin karbar na goro da Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka FBI ke yi masa.

Comments