Main menu

Pages

ABBWN DA KE KAWO QARANCIN RUWAN NONO GA MAI SHAYARWA

 


KARANCIN RUWAN NONO [BREAST MIlK]

Abubuwa kalilan wani lokacin Kän kawo karancin samun wadataccen ruwan nono dakan sa dole sai an hada da baiwa yara jarirai madara. 

A wasu matan suna da karancin karsashin prolactin inda hakan kansa nonon bai samuwa a wadace.

Wasu lokutan kuma akan ga ruwan nonon akaron farko amma sai daga baya ace ya dauke, irin Wannan Kän faru ne da yawa sakamakon sakacin iyaye mata.


Ga muhimmai daga cikin abubuwan dake jawo karancin ruwan nono:-

1- Rashin shayar da jariri nono akai akai. Ya zamto kirika tunanin tunda ba kuka yake ba bai da bukata, ko kuma ma ko yana kukan kirika jin ke ya fiye tsotso da yawa. A'a tsotso baya yawa kuma masu yawan shayarwa keda kanki zaki ga sunfi yawan ruwan nono, don haka in kina son magance matsalar ki shayar dashi iya iyawa akai akai.


2- San nan inya zamto kina hada shayarwa da aikace-aikace. Duk sanda ya kasance yaron kina shan nono kina Mika hannu kina wani abun nonon na kuccewa daga abakinsa hakan nasa arasa sensational breast sucking wanda tsotsowar da yake shi kesa glands din dake samar da ruwan nonon ke kara kaimi. Don haka an so ki natsu ki zauna.


3- In ya zamto nono daya kike bashi ko shiki kafi bashi to wannan matsalar ka iya shafar level na Samar da ruwan nonon duk breast din. Don haka ki kasance kina canza mai nono kowanne ya kama akalla Sau bi-biyu ko uku a duk kan zaman shayarwa.


4- ki dena matsar ruwan nono kina zubawa a feeder ko bottle kina bashi ko kina bari a gida ana bashi saboda kina zuwa wajan aiki hakan ma na kawo karancin ruwan nonon saboda duk abinki babu kamar ace yaronka na kama nono hakan na taimaka ma jikin ki sosai kuma shi zaisa a sami wadataccen ruwan nono.


5- Anso a watanni shidan farko ya zamto zallan ruwan nono kike bashi hakan na taimaka wa a sami ruwan nono awadace kuma kike bashi akai akai akalla ko bai yi kuka ba digestion din Jira jirai bai wuce awa daya da minti hamsin (1hr, 50mint) jikinsu kan kuma bukaci nono.


6- Iya bayar da nonon kansa ya zamto bakin yaro ya rufe shacin bakin nan na nono rijif sosai, hakan na taimakawa.


7- A al'adance mutane Hausa Fulani na da dabi'ar damawa mai jego kunu ko wani liquid product safe da yama, munsan ga masu hawan jini da matsalar zuciya akan hanasu amfani da kanwa, tabbas domin tana raising pressure to sai de ga wadan da suke lafiya kanwa kwai sinadarin potassium wannan yakan taimaka wajen habbaka ruwan nono Shima.


8- Idan duk wadancan anyi amma kila yan  biyu ne to akan kai ga rubutawa uwa magani dangin su ANTIEMITEC dai dai da kirar jikinta donsu taimaka mata.

Comments