Main menu

Pages

TARIN SIRRIKAN DA KE TATTARE DA GAWAYI DA BA MU SANI BA







 WASSU DAGA CIKIN AMFANIN GAWAYI (CHARCOAL)!

Gawayi yana daga cikin amfanun kasa wadanda ba'a damu dasu ba a gidajenmu koma bayan amfani da akeyi dashi wajen girki, gasa masara, hayaqi, shan lope, kunna turaren . 


Duk da hakan, idan kana buqatar agaji ko taimako na gaggawa, gawayi wani abune daya kamata Kana tare dashi a kowani lokaci.  Ba lalle bane kasan hakan, ammana Gawayi kamar yadda kake buqatar sauran magunguna kusa da kai, haka kake buqatar gawayi domin yana tsotse guba. 


Idan baka damu da amfanin gawayi ba a baya, toh yanxu dama ta samu da zaka damu da amfanin shi gareka. 


Ga wassu daga cikin amfanin gawayi ga Al'umma: 


1. GAWAYI YANA HANA WARI: 


Shin takalmanku suna wari? Ku samu gawayi ku sanya a cikinsu. 


Shin Kuna fama da wani irin wari a dakinku? Ku jefa gawayi a inda kuke tsammanin warin na fitowa.


Shin fridge dinku yana wari? Nemi gawayi ko qwalli guda ne ka sanya aciki. 


Shin jikinku na wari haka kawai ko warin qashi?  Kuyi powder na gawayi Kuna amfani dashi. 


2. YAKAN HANA ABINCI MUSAMMAN GANYAYYAKI BACI 


Idan kuna buqatar ganyayyanki ku su zama fresh koda yaushe, kuyi jiqo na gawayi saiku sanya ganyayyankin aciki. 


3. CIRE GUBA DAGA ABINCI: Idan kuna da kayan abinci ko ganyayyanki da kuke tsammanin an sanya musu maganin qwari da zai muku illa, ku sanyasu a kasar gawayin na dan wani lokaci kuyi amfani da abunku,  hakan zai cire guban. 


4. GAWAYI NA TAIMAKAWA WAJEN HASKAKA HAQORI

Idan kuna buqatar haqwaranku suyi haske, ku manta da duk wadannan tallukan na T. V. Ku nemi gawayi ku daddaka shi, sannan Ku nemo ashuwakinku ko wani abu mai Kama da hakan Kuna goge haqorinku dashi na sati, Insha Allah zaku samu nasara.  


5. YANA GYARA MIYAR DA TAYI TSAMI 

Idan miya ta 6aci, a samu gawayi a jefa aciki sannan a maida miyar kan wuta tayi dumi. Cikin ikon Allah gawayin zai dauke wari ko tsami da miyar keyi.


6. GAWAYI YANA RAGE MAYE. idan kasha wani magani daya sanyaka maaye, ka nemi gawayi ka tauna ko ka jiqa kasha ruwan. Insha Allah za'a dace. 


7. GAWAYI YANA BUSAR DA CIWO

Idan kanada wani wanda ciwo ya addabeshi har likitoci ke tunanin zasu yanke wajen ciwon,  kada hakan ya daga maka hankali, ka nemi gawayi Ka daddaka shi sannan kana xubawa akan ciwon. Hakan zai tsotse dukkanin guba dake ciwon kuma zaisa ciwon ya warke da wuri. 


8. GAWAYI KAN TAIMAKA WAJEN TACE RUWA

Idan ruwa ya gur6ata, ka nemi gawayi Ka jefa aciki, Kada kadamu da launin ruwan, babu abinda zai maka domin zaka iya cin gawayi don yafi wadannan kajin turawa da kake ci amfani. 


9. YANA GYARA FATA. 


Kana fama da pimples, kazuwa ko kuma qesbi ko kuma kowani irin cutar fata? Ka nemi gawayi ka daddaka sannan Ka kwa6a gawayin, sannan kana mulkawa a jikinka ka bari na wassu mintuna kafin ka shiga wanka. Idan kayi haka na sati Insha Allah zaka samu waraka. 


10. YANA FITAR DA DATTI. 


Idan Kuna fama da datti a kitchen ko wani waje, ku nemi gawayi  kuyi amfani dashi a wajen da dattin yake, Insha Allah zai cire wannan datti. 


11. Idan cikinka ya kumbura ta dalilin cin wani abu ko shan wani abu, ka nemi gawayi ka tauna ko ka daka ka jika kasha ruwan.  


12. YANA RAGE KITSE 

A samu gawayi a daddaka sannan a jika da tsamiya ko lemon tsami, yana rage kitse sosai. 


13. GAWAYI YANA MAGANIN ULCER

Idan Mutum yana tauna gawayi lokaci bayan lokaci Insha Allah  za'a samu nasara. 


Allah Ya bamu ikon kulawa da lafiyar mu Ya kuma kara mana lafiya da abinda lafiya zataci

Comments