Main menu

Pages

WANNAN SHINE DALILIN DA YASA MANSURA ISA DA SANI DANJA SUKA RABU.

 


Dalilin Rabuwar Sani Da Mansura:Ya Kara Aure A Sirance


Wasu Majiyar Zuma Times Hausa da ta hada da Mujallar Fim sun bayyana cewa tsofafin jarumai na Kannywood, Sani Danja da Mansura Isa sun dade da rabuwa inda Mansura ta koma gidan hanya da zama tare da 'ya'yanta hudu.
An ce dalilin rabuwarsu na da alaka da auren sirri da Sani Danja ya yi a Kaduna ba tare da sanin Mansura ba har sai da matar ta haihu.
Majiyar ta ci gaba da cewa Mansura ta yi alkawari ba za ta ba shi ko daya daga cikin rayan ba.
Wadanda ke kusa Mansura sun bayana cewa ba wannan ne farko da Sani Danja da Mansura suka rabu ba don ya taba sakinta a baya.
Zuma Times Hausa ta samu karin bayani da ke cewa Mansura ta gaji da halayen mijinta ne don saki mata hidimomin gida da ya ke yi inda ta ke daukar dawainiyyar tafiyar da al'amuran gidan.
Bincike ya nuna cewa Mansura dai mace ce mai kokarin neman na kanta da taimakawa marasa karfi.


To mina fata Allah Ya shirya tsakaninsu.


Duk kokarin da majiyar ta yi ta don jin na bakin ma'auratan ya ci tura.

©Zuma Times Hausa

Comments