Main menu

Pages

MATA KU KOYI YADDA AKE HADA HADADDIYAR GUMBA DA KANKI

  



   HADIN GUMBA
 

Kunnuwan bagaruwa

Agallashe 

Minannas 

Kanun fari

Gero 

Sugar


Zaki hada kunnuwan bagaruwarki da agallashe ki daka su sudaku sosai sai kisa matankadi  ki tankade su suyi laushi sosai ki aje gefe saiki dauko kanunfarinki da minannas masu yawa zakisa sannan kidauko tuntuben halshe shima ki hada su guri daya ki dakasu su daku sosai. 



Saiki tankadesu suyi laushi sosai suma ki ajiyesu gefe sannan shima geronki ki surfashi yasurfu saiki wanke idan ya bushe saiki kaishi nika maki shi, kitankade shi kicire dussa saiki samu tukunyarki ki dorata awuta saiki zuba suganki yaita dahuwa idan yadahu zaki gane idan yadahu zaita fidda kunfa sosai shine alamun yadahu 




kuma zaki iya debo dan kadan a cikin cokali idan kikaga yadaskare bai dahu ba idan kuma kinkaga yana yauki to yadahu saiki hade kayanki gaba daya guri daya ki yamutsasu sai kinga sun hade sosai sannan ki zuba su achikin wannan sugan



 kisa muchiya kina tukawa kina tukawa sai kinga kayan sun hade da wannan sugan sannan kisamu bokitinki mai tsafta kizuba achiki kisamu madara ko nono kina damawa kinasha himmm sister lafiya laune fa 



Comments