Main menu

Pages

HANYOYI GUDA 9 DA ZA A BI DON MAGANCE KOWANNE IRIN CIWON KAI.

 Magungunan Ciwon Kai Na Musulunci
 

Ciwon kai yana daga cikin ciwuka irin na yau-da-kullun wadanda suka addabi Jama’a. Mafiya yawan mutane su kan yi ciwon kai a kalla sau biyu ko sau uku, ko fiye da haka Lokaci zuwa lokaci.Shi yasa likitoci suka lalubo muku wasu fa’idodi Mujarrabai wadanda inshaa Allahu za su amfanar tare da taimakon Allah idan anyi amfani da su.
1. KANUMFARI : Wanda ya ke fama da ciwon kai irin na Mura ko sanyi, ko Jiri, ya nemi garin Kanumfari cokali biyu ko Uku, ya dafa shi da ruwa. Bayan ya dafu sai a sanya ruwan Khal cokali biyu, a sanya Sukari sannan a sha. In sha Allahu koda majina ce ta daskare a cikin Kirjin mutum to za a samu sauki da izinin Allah.
2. KABEWA : Kabewa idan aka dafa, aka samu ruwan ta aka hada da Sukari aka rika sha. In shaaAllahu yana magance yawan ciwon kai.


Kuma Namiji wanda yake fama da rauni wajen biyan bukatar iyalin sa, ko kuma Mace wacce take fama da matsalar daukewar sha’awa, ko Bushewa za su samu sauki. Haka nan mutumin da zuciyar sa take yawan bugawa da karfi shi ma idan yana shan ruwan kabewar zai samu sauki in shaaAllah.
3. HABBATUS-SAUDA' : Ka samu rabin kofi na ‘ya’yan Habbatus-sauda', Kanumfari cokali biyu, Yansun ma rabin kofi. A hada su a daka a turmi. Sannan a rika diban cokali biyu ana dafawa da ruwa kofi daya. Idan ya dahu sai a bar shi ya huce, sannan a zuba zuma, a rika sha.

Masu ciwon kai, Masu Olsa (Ulcer), Masu hawan Jini, Masu ciwon kirji, Masu tsakuwar koda, idan suna shan wannan za su samu lafiya da izinin Allah. Za a rika sha safe da yamma ne.
4. LEMON ZAKI : A samu bawon Lemu a yanyanka shi kamar cikin kofi guda, a dafa shi da ruwa kofi biyu. Idan ya tafasa sai a sauke. A tace da rariya sannan a sanya zuma a rika shan sa safe da yamma.

Masu Ciwon kai da masu fama da kumburin ciki ko rashin narkewar abinci za su samu lafiya.
5. NA’A-NA’A : A samu ganyen Na’a-Na’a, Ganyen Raihan, a dafa su tare da kanumfari a rika sanya zuma, ana shan ruwan da dumin sa, sannan a rika goga ganyen akan goshin marar lafiyan.

Wannan maganin Ciwon kai ne sadidan, kuma yana magance cutar Kumburin jiki, yana magance ciwon sanyi na mata, yana magance ciwon daji (Cancer). In shaaAllahu.
6. SANA-MAKKIY : Cokali uku na sanamiki, Cokali uku na garin Habbatus-Sauda, Cokali biyu na chitta a hada su a dafa da ruwa kofi biyu sannan a sanya sukari a rika sha safe da yamma. Sannan a rika shafa MAN CHITTA (Ginger Oil) akan goshin marar lafiyan.

In shaaAllahu kai zai daina ciwo. Idan kuma Jiri ne ko Hajijiya shima za a samu lafiya in sha Allah.
7. MAN HABBATUS SAUDA : A rika shafawa akan marar lafiyan in shaaAllahu kan zai daina ciwo. Amma za a rika maimaitawa safe da rana da yamma.
8. MAN RAIHAN : A hada man raihan da Man Hasa-lebban, tare da turaren Wardi a hada waje guda a rika shafe jikin marar lafiyan baki daya. Bayan an karanta Fatiha 7, Ayatul kursiyyi 7, Suratul Feel 11, Qul Huwallahu 11, Falaki da Naasi 11 a tofa a cikin wannan hadin. In shaaAllahu wannan maganin ciwon kai ne sosai musamman irin wanda Shaidanun Aljanu suke haddasawa. Kuma yana magance ciwon jiki ko shanyewar gabobi irin wanda Aljanu ke sanyawa.
9. FUREN ALBABUNAJ : Idan aka tafasa cokali biyu, ana shan sa safe da yamma kamar shayi, in shaaAllahu za a ga abun mamaki wajen samun waraka daga ciwon kai, ciwon koda, rashin barci, faduwar gaba, makalewar fitsari, da sauran su.


Comments