Main menu

Pages

CIKAKKEN BAYANI AKAN ZAZZABIN TYPHOID, ABIN DA KE KAWO TA DA HANYAR MAGANCE TAZazzabin Typhoid, Alamominta da Abinda ke kawota, da Yadda za a MagancetaZazzabin typhoid ya kasance zazzabi mai wuyar sha’ani ta yanayin hawan shi da saukarshi gami da yadda yake haye karfin magunguna ta yadda zaka ga basa tasiri akansa. Ku biyo ni sannu a hankali don samun bayanan daya bayan daya.
Alamomin zazzabin typhoid

Wasu daga cikin alamun dake nuni da yiwuwar cewa ka kamu da wannan zazzabi na typhoid sun hada da:

√ Zazzabi mai matsanancin zafi

√ Ciwon kai ba kakkautawa

√ Ciwon ciki

√ Rasa jin dadin duk wani nau’in abinci

√ Ciwon wasu sassa na jiki dadai sauransu..


Menene ke haddasa ciwon zazzabin typhoid ? 

Allah shine mai kare bawanShi daga dukkan wasu cututtuka, idan kuma yaso sai ya jarrabeka da ciwo don hakan ya zama kaffara a gareka. Binciken da masana harkar kiwon lafiya suka gudanar ya nuna cewa wasu nau’o’i ne na kananun halittu ( nau’in bacteria ) na Salmonella typhi da kuma Salmonella paratyphi wadanda mafi yawan lokuta ana samunsu ne a cikin ruwan sha mara tsabta ko ta hanyar cin gurbataccen abinci a wani lokacin kuma mutane kan iya dauka a sakamakon sakaci daga mai dauke da wadannan kwayoyin cuta musamman idan yayi bayan gida (kashi , ba haya, bayan gari) ba tare da ya wanke hannayensa da kyauba.
A yayin da mutum yaci wani abinci ko wani abin sha mai dauke da wannan kwayoyin cuta to sukan tafi ya zuwa yan hanjin mutum daga nan kuma sai su watsu zuwa cikin jinin mutum inda zasu sami damar yaduwa zuwa hantar mutum da kuma wasu sassa na jikin dan adam daga nan kuma sai su cigaba da hayayyafa.


Bincike ya nuna cewa ba daga shigar kwayoyin cutar suke haddasa ciwo ba, sukan dauki sati daya zuwa biyu kafin mutum ya fara ganin alamomin ciwon suna bayyana a gareshi.
Yadda Za’a magance wannan ciwo

Duba ga yadda zazzabin typhoid ya kasance mai wuyar magani ta yanda zaka ga cewar mutum nata faman shan magunguna kala-kala amma kamar ma yana kara rura zazzabin ne yasa masana harkar maganin gargajiya sukayi gwaji akan ciyawar Rai dore wacce takan fito a gefen gari tare da tafasa da kuma wasu sauran ciyayi.

Hanyar farko

• Da farko dai mutum zai samo ganyayyakin rai dore din da yawa sannan sai a wanke da ruwa mai kyau.


• Sai a zuba ganyayyakin a turmi sannan a dan jajjaga su da tabarya.


• Sai a kwashe a zuba ruwa mai tsabta adan barshi ya jika sannan sai a matse shi sannan a tsame daga bisani kuma sai a tace ruwan.


• Bayan haka sai a sami kofin tea ko kuma wani dan madaidaicin kofi sai a zuba daidai wanda za’a iya shanyewa sannan sai a zuba rabin gwangwanin madarar peak ko luna ta ruwa sai a shanyen gaba daya.

So biyu za’a sha a rana, wato safe da yamma na kamar tsawon kwana uku.Hanya ta biyu

Idan ba a sami damar daka ganyayyakin ba to za’a iya dafawa sannan sai a tace a barshi ya hucce sannan sai a zuba madara asha kamar yadda nayi bayani a baya.Baya ga maganin ciwon typhoid da rai dore keyi, bincike ya nuna cewa yana kashe kwayoyin Plasmodium musamman falcifarum dake kawo zazzabin malaria na cizon sauro wato dai baya ga kasancewar rai dore maganin typhoid to kuma yana maganin malaria.


Wannan shine dan takaitaccen bayani dangane da amfanin rai dore wajen magance zazzab in typhoid. 


Ina rokon Allah (SWT) da ya bawa duk marasa lafiya dake kwance a gida ko asibiti lafiya, mu kuma masu lafiyar ya Kara mana koshin lafiya gami da kwanciyar hankali.


Ga wani hadi wanda yake Mujarrabi ne in shaAllah idan anyi shi za'a dace :


1. Ganyen Dogon yaro. 

2. Ganyen Guava. 

3. Ganyen Gwanda.

4. Ganyen 'Doddoya.

5. Tafarnuwa (Manya guda 5 ko 7 )

6. Citta. 

7. Kanumfari.

8. Kimba. 

9. Albasa (2 Madaidaita) 

10. Lemon Tsami (5).


11. Zuma (Optional).


 


YADDA ZAKU HADA:

Ka samo wadancan ganyayen (from 1 - 4) kowanne kamar cikin kofi guda.


Sannan a zuba sauran kayan hadin (from 5 - 10) daidai misali. Amma ana so tafarnuwa da citta sufi yawa.


A zuba ruwa galon daya da rabi, a dafa sai ya kusa tafasa (Close to boiling point) sai a janye wutar, a barshi ya Qara minti goma sannan ka saukeshi.


Idan ya huce sai ka rika diban kofi guda kana sha sau uku (Safe, rana, da dare).


Idan Qaramin yaro ne (daga dan shekara 3 zuwa 7 ) za'a bashin rabin-rabin kofi ne. (¼). Idan kuma ya kai dan shekara 10 zuwa 15, za'a bashi rabin kofi ne.


Idan Zazzabin Malaria ne, za'a yi kamar kwanaki 4 ana sha. Idan kuma Zazzabin Typhoid ne, za'a yi kwanaki 7 ana sha.


ABIN LURA : KODA BAKA SAMU DUKKAN KAYAN HADIN BA, ZAKA IYA YI DA WADANDA SUKA SAMU AWAJENKA. KUMA IDAN RUWAN YA FARA QAREWA, ZAKA RIKA QARA RUWA KANA SAKE DUMAMAWA.


Allah yasa adace


Comments