Main menu

Pages

WANNAN SUNE ILLOLIN DA RASHIN SHAN ISASSHEN RUWA KE HAIFARWA




 ILLOLIN DA RASHIN SHAN RUWA ISASSHE KE HAIFAR WA:


Lokocin sanyi dayawa daga cikin mu bamu damu da shan ruwa ba kwatakwata.


Alhalin munsan dukkan halittun jikin mutum na bukatar ruwa domin gudanar da aikinsu yadda ya kamata.


Ga kadan daga cikin matsaloli da rashin Shan ruwan akan lokoci zai iya kawo maka:

1. Tamushewar fata da saurin tsufa

2. Rashin iya narka da abincin da aka ci da wahala wajen fitar da bahaya

3. Gyambon ciki. 

masu Ulcer shida ne dan tafi tashi lokacin sanyi fiye da lokacin zafi da kaso 75 cikin 100

4. Rama

5. Ciwon gabobi

6. Zafin jiki

7. Rashin kuzari da saurin gajiya

8. Ciwon koda

9. 2. Hatsarin kamuwa da cutar mutuwar rabin jiki

10. Ciwon kai


Ga bayanin Dr. Jide Owolana akan rashin shan ishesshen ruwa :


"Karancin shan ruwa yana iya haifar da canjin dabi’a, ya na rage kaifin basirar dan adam, sannan ya na haifar da cutar mantuwa, da kuma sa mutum da dinga jin radadi fiye da in yana yawan shan ruwa, don haka yakamata mutane su kiyayi rashin shan ruwa




AMFANIN SHAN RUWA DA SAFE KAFIN ACI KOMAI:;


Shan ruwa da zarar an tashi da safe yana da matukar amfani ga lafiyar dan adam. masana fannin kimiyya sunyi bincike akan hakan.masu bibiyar mu a wannan gida mai albarka saiku biyoni sannu ahankali donjin amfaninsu:


1.ciwon kai

2.ciwon jiki

3.daidaita tsarin bugun zuciya

4.amosanin gabbai

5.farfadiya 

6.daidaita jikin da yawuce kima

7.asthma

8.ciwon koda

9.cutukan dake cikin fitsari

10.ciwon suga


Kadan daga ciki kenan....


Don haka a dage da shan ruwa saboda amfaninsa ga jikinmu.

Comments