Main menu

Pages

 
 🌿 MIYAN ZOGALE 🌿


INGREDIENTS

🥗Tattasai🌶️

🥗Tumatur🍅

🥗Albasa🧅

🥗Attaruhu🌶️

🥗Zogale🌿

🥗Gyada🥜

🥗Nama🥩

🥗Ganda🥠

🥗Kifi🦈

🥗Tafarnuwa🧄

🥗Gyadan qamshi🥔

🥗Manja

🥗Maggi

🥗Curry

        

         **PROCEDURE**

Dafarko uwargida zata gyara kayan miyanta saitayi blending dinsu,saita juye a mazubi Mai tsafa,sannan sai uwargida ta gyara zogalenta,ta wankeshi ta tsaneshi a colender, uwargida zata gyara gyadarta tasoyata sama-sama, saita murje bawon dake jikin gyadar, sai uwargida ta daka yar citta da gyadar qamshi,saita zuba wannan gyadar data gyara, sai kii daka dakyau harsai kinga tayi laushi, saiki dauko tafarnuwanki ki bareta kizuba Akan wannan gyadar dakika daka, uwargida zata cigaba da dakawa harsai kinga yafara alamun zau fitar da mai,saiki zuba mazubi mai safta,then uwargida Zaki dauko tukunyarki mai tsafta saita dorata akan wuta saiki wanke nama kizuba kibarshi yadahu, saiki zubawa busashen kifinki ruwan zafi bayannkin gyarashi,saiki wankeshi tas,dama already uwargida ta gyara da tsaftace gandarta,saki dafashi yadahu sosai, sai uwargida tasauke daga kan wuta,sannan uwargida zata dorawani tukunyan Akan wuta kizuba manja,kisoya,saiki zuba kayan
 miyanki,kisa yar kanwa aciki sabida gudun tsami,kibarshi yadahu sosai,saiki kawo gandanki ki zuba kibarshi yadahu sosai saiki kawo kifinki dackika jiqa ki zuba,sannan nama shine na qarshe,saiki juya dakyau harsai kinga komai yahade jikinshi, saiki kawo wannan gyadar dakika daka,ki kwabata da ruwa,saiki zuba akan wannan kayan miyan naki nakan wuta,itama kijuyata ta juyu,sabida gudun kada yayi miki kamu,
sannan saiki barshi yadahu for some minutes, then saiki saka Maggi da curry,ki juya dakyau, kibarshi yasamu at least 4 to 5 minutes, then saiki dauko wannan zogalen da kika wanke tun da farko,saiki zuba,kijuya ko'ina da Ina,then kirufe tukunyan kibarshi yadahu sosai,saiki sauke

     

NOTE:-zaki iya yin miyan kizuba daddawa,Amma bada yawaba,musamman idan na busashen Zogale 🌿 zakiyi,yana dadi sosai
                  MIYAR ALBASA

 


INGREDIENTS

*Nama tsoka zalla

*Albasa

*Attarugu

*Tumatur

*Mangyada

*Curry

*Thyme

*Maggi

*Salt

 


PREPARATION

     Da farko ki tafasa nama, albasa, spices, seasoning idan naman ya dahu saiki kwashe ki daka saiki yanka albasa mai yawa misali manya guda 3 tumatur 2 attarugu 3 but, albasa zaifi kyau kiyi grating ki soya mai ki zuba albasa da jajjagen tumatur, attarugu kisa maggi,salt,curry idanta dahu saiki xuba dakakken naman saiki rinqa juyawa kamar 5mnts saiki sauke shikenan asha dadi lfy            Miyar Ayoyo

Abubuwan hadawa

Albasa

Attarugu

Nama

Tumatir kadan

Danyar tattasai kadan

Daddawa

Ayoyo

Curry

Maggie

Gishiri

Kanwa 

Mai

Wake


Yadda ake hadawa

Da farko za ki hura wuta ki daura tukunya ki sa mai kadan, ki yanka albasa ki zuba, ki sa tumatir, attarugu, danyar tattasai, da nama ki soya miyar da kyau.


Daganan sai ki zuba ruwa ki sa wake, maggie, curry, gishiri, daddawa, da kanwa kadan ki rufe ki bari ya tafasa waken ta nuna.

Idan ruwan ya yi dai dai miyar da ki ke so sai ki yanka ayoyo ki zuba ki rufe ki sauke bayan mintuna kadan.

Karin bayani


Ki rage wuta bayan kin zuba ayoyo in ba haka ba miyar ki ba za ta yi yauki ba

Kada ki cika tumatir da danyar tattasai, in su ka yi yawa shima zai hana miyarki yin yauki sosai.

Acii daddii lfy.

Comments