Main menu

Pages

HUKUNCIN KAYYADE IYALI A MUSULUNCE

 




HUKUNCI KAYYADE HAIHUWA (FAMILY PLANNING)


Abubuwan da ake amfani da su wajen kayyade iyali sun kasu kashi biyu


 1. Wanda zai hana daukar cikin kwata-kwata, a nan bai halatta ba, saboda ya sabawa manufar shari'a na yawaita al’uma, kuma ‘ya’yan da take da su za su iya mutuwa sai ta koma mai wabi.



 2. Sai wanda za a tsayar da shi ne na dan wani lokaci, kamar mace ta zama tana yawan haihuwa kuma cikin yana wahalar da ita, sai ta yi nufin ta tsara haihuwarta ta yadda za ta haihu duk bayan shekara biyu ko makamancin haka, to wannan ya halatta




 In dai miji ya bada izini kuma ba zai cutar da matar ba, dalili akan haka shi ne sahabbai sun kasance suna azalu a zamanin Annabi s.a.w. don kar matansu su dauki ciki, kuma ba’a hana su ba, kamar yadda Bukari ya rawaito daga hadisin Jabir mai lamba ta: 4911.



Abin da ake nufi da azalu shi ne idan namiji yana saduwa da matarsa idan ya ji zai kawo  sai ya fitar da gabansa ya zubar  a waje.



Allah Shine magi sani, Allah Ya shiryar damu hanya madaidaiciya. Ameen

Comments