Main menu

Pages

GASHINKI NA YAWAN KAKKARYEWA, TO GA NAGANI INSHA ALLAH
HANYAR GYARA GASHI DOMIN HANASHI KARYEWA DA CIREWA


_Hanyar gyara gashi mai inganci. 

Akwai wani mai daake cemasa lJALASSIRIN Insha Allah zaki iya samun sa wajen masu sayar da kayan shafe shafe na mata. Amma Wanda take a Kano zatafi saurin samu, domin kai tsaye zaki iya samun sa a ALPHEN STORE Kano,_

Za'a samo shi da kuma  ZAIT SIBAR.

Zaki samo  ZAIT JUJJUBA.

Insha Allah duka zaki iya samu anan ko dai a sauran wasu manyan gurare._Idan aka samo su zaa hada waje daya sai kuma azuba ruwa kadan sai amotsa shi sosai ta yadda zai hade,daganan zaki shafa akai bayan kinwarware shi zaki barsa zuwa minti 20 sannan zaki wanke.Sannnan zakiyi kamar Sati (3)Koda ba'a jere ba.To insha Allah cutan dayake sanyawa gashi yarika bushewa yana karyewa zai rabu dake.Allah kasa mudace ameen.Bayan haka mayuka wadanda suke kara ma gashi kyau, duhu, haske, tsawo sune kamar haka:

_(1)Man habba

_(2)Man zaitun mai kyau

_(3)Man alayyadi

_(4)Man hulba

_(5)Zait lauz halawi

_(6)Man simsim_

_(7)Man lalle_wato zait Henah.

_Wadannan su za'a hada waje daya za'a shafa baza'ayi kitso ba har sai bayan minti 30-60._Sannan idan nasama yayi wahalar hadawa mai Jalassarein.

     _To sai kibi wannan hanya na biyu Zaki samo lalle ko danye, ko bushasshe, amma banda gari,sai kihada da yayan hulba, kihada Albasa, kihada tafarnuwa sai kitafasa akalla minti 20-30 sai kisauke kitace


 bayan ya kusa hucewa yer uwa kamar yadda zaki iya amfani dashi bazai cutarba, daganan dama antsefe kai sai awanke kai dashi sai abarshi zuwa wani lokaci amma ana bukatar za'a lullube kan da leda, sannan awanke._To bayan yasha iska wadannan mayukan Habba,hulba,zaitun,lauz,simsim su zaki shafa bazaa kitse kanba har sai bayan minti 30-60.

.

_Insha Allah idan kinbi wannan hanya koda kanki yazube ya koma irin namaza insha Allah gashi zai Tohoo kuma yayi yawa, yakara tsayi, yayi duhu, yayi haske, wasu dadama mun basu sunjarraba kuma sun dace kwarai da izinin Allah._Amma kamar wadannan mayukan idan ana shafa su wajen yin kitsu to suna taimakama gashi yawar ware,kuma yakara kyau da santsi,yayi duhu,kuma yarika kara tsayi,musamman idan ansami masu kya._Sanann man *Jalassaren* shi kadai yana magane karyewar gashi._

.

        ​

Comments