Main menu

Pages

AMFANIN GANYEN MANGORO, DA MAGANIN BASIR KOWANE IRI NE DA YARDAR ALLLAH




AMFANIN GANYAN MANGORO:


Ganyen Mangwaro ya kunshi sunadarai masu tasirin gaske ga lafiyar dan Adam wajen kawar da wasu cututtuka da suka saba addabar al’ummar musamman a wannan zamani. Ire-iren wannan sunadarai sun hada da:

- Alkaloids

- Phenols

- Flavonoids

- Saponins

- Tannins

- Calcium

- Magnesium

- Potassium

- Phosphorus

- Sodium

- Copper

- Zinc

- Cadmium

- Ascorbic acid

- Riboflavin

- Niacin

- Thiamine


A sakamakon wannan arziki na sinadarai da Allah yayiwa ganyen mangwaro Yana maganin wadannan cututtukan: 



1- Ciwon Suga

Ganyen mangoro yana daidai ta suga, sabida yana dauke da sinadarai masu saka jiki ya saki insulin.


Ana iya jika ganyen magwaro a cikin ruwa ya  kwana sai ayi amafani da shi yana taimaka wajen daidai ya suga.


Haka Kuma za'a iya barin sa ya bushe sannan a maida shi gari adinga amfani dashi domin daidai ta suga.



2- Hawan Jini

Kasancewar ganyar mangiro yana dauke da sinadaran vitamin hakan zaisa ya kona cholesterol mara amfani a jikin mutum, sannan ya daidai ta jinin mutum.



3. Matsalarar Koda

 dafa ganyan mangoro kamar shayi a dinga sha da safe a matsayin abincin farko yana kawar da matsalar Koda, kuma yana narkar da tsakuwar koda tare da tsarkake ta daga cututtuka.



4- Matsalar Kirji ( Respiratory Track Infection)

Ana iya dafa ganyan mangoro kamar shayi sannan a saka zuma a ciki ana amfani da shi ya saukake matsalar tari da rike kirji.



5- Cutar Atini

Akan kwankwadi garin ganyen Mangwaro da aka jika da ruwa wajen samun waraka daga cutar atini ko da kuwa mai zuwa ce da fitar jini.




MAGANIN BASUR KOWANNE IRI.


Duk mai fama da matsala ta basir ko dattin ciki ko cushewar ciki ga wannan ingantacciyar hanya wacce zaibi domin samun sauki da warama.


1. Lemon-tsami guda uku  

2. Tsohuwar-tsamiya guda uku  

3. Jan-gauta guda uku  

4. Barkono guda biyar  

5. Sabulun sha kamar girman lemon tsami.


Dukkan wadannan abubuwa In aka tashi sai a hade su wajedaya, a jika, su kwana. Kullum sai a tsiyayi rabin kofi a sha da safe kafin a ci abinci. Ana diba ana kara ruwa, har sai ya salamce sannan a zubar.


Wannan magani ne na Basur sosai. Indai ka hada shi zai warke, ka rabu da shi da iznin Allah.



Comments