Main menu

Pages

SABON SALON YAUDARA. MATA A KULA

ABINDA YA FARU DA WATA BAIWAR ALLAH KENAN


Da Sigar Aure Ya Zo Mini Ashe Zina Yake Son Yi Dani:

 Mai Labarin ta fara ne kamar haka;

Shekaru na yanzu sun kai 24 da haihuwa. Daidai gwargwado ina kiyaye addini da kuma tsoron duk wani abunda zai sani na sabawa mahalicina.Mun hadu dashi ne wani bukin kawar kawata. Daga wannan lokacin soyayya ta kullu a tsakanin mu. Da farko ban bashi mahimmanci ba. Ganin yadda ya nuna da gaske yake yasa har na kamu da sonsa.Tun a farko da zancen aure ya zo mini. Kuma ya nuna mini idan har na amince shi a shirye yake da mu yi aure. Ganin yana da mata daya kuma da yara biyu duk da yake yana da karancin shekaru yana kuma da aiki mai kyau yasa ban dau lokaci wajen amince masa akan zan aure shi ba.Lamarin namu ya kai har na gabatar dashi a wajen iyayena a matsayin wanda zan aura. Kuma a iya binciken su suka tabbatar mini da sun amince na aure shi amma tunda saura mini shekara guda na kammala karatun da nake yi na difiloma ya hakura har sai na gama. Ya kuma ce babu damuwa.Da farko bai nuna mini yanada wata manufa na daban ba a game dani. Kamin shi samari da dama sun nuna mini shaawarsu na son aurena. Amma da sun soma zuwa sai kuma naga sun shigo da wasa ko kuma neman iskanci. Hakan yasa ko lokacin da shi ma yazo banyi saurin sakin jiki dashi ba.Ya bini yadda nake so babu zance ko kalamai na banza a tsakaninmu. Bai taba nuna mini akwai wata sha'awa ta daban da yake mini ba idan banda na aurena. Hakan yasa na kamu da sonsa matuka. Kusan kullum sai mun yi hirar sama da awa guda kamin muyi barci ganin shi ba a garin da nake yake aiki ba. Na kamu da sonsa fiye da misali. Har nake ganin bazan iya rayuwa ba idan har bada shi ba.Ganin yadda cutar Corona tazo ta dakatar da karatun mu. Hakan yasa iyayena suka yanke shawarar nan da watannin uku masu zuwa a daura mana aure. Don haka na isar masa da wannan sakon ya kuma amince. Sai dai daga wannan lokacin sai na soma ganin sauyi na rashin kamalar dana san shi dashi a farko. Ya soma tura mini hotunan batsa, daga nan kuma sai bidiyo. Tun bana so har na soma so. Muka dawo muna hiran bidiyo kol sai yayi tsirara nima hakan muyi ta wasa da al'auran mu. Hakan muka yi tayi kusan wata guda muna yi.Wata rana muna hira sai yace mini shifa gaskiya bazai iya auren macen da bai yi zina da ita ba. Dole sai ya taɓa yaji yadda nake. Duk kokarin da nayi domin canza masa wannan tunanin ya faskara. Ga shi kuma a gidan mu ana bukatar ya turo a saka rana. Hakan yasa daya matsa mini na amince masa zan bashi haɗin kai kamar yadda ya bukata.


Musamman yazo weekend domin yayi zina dani sai kuma ya tura a ga iyayena.


Hotel ya kama mana mai tsada. Muka yi mahada yazo ya daukeni. Tunda kusan karfe biyu na rana da muka shiga bamu fito ba sai bayan sallar isha'i. A tsawon wannan lokacin yadda yaga dama haka nan yayi dani amma da muka tashi barin ɗakin otel din ne yayi mini maganar da har abada bazan manta ta ba."A hakan kike so na aureki bayan duk kin raba gindin ki a waje. Dubi yadda na sameki sai kace wacce ta taba aure. To ki sani daga wannan lokacin kada ki sake cewa kin sanni ko a hanya kika ganin kika mini magana sai na wanka miki mari. Duk uban da zaki fadawa nayi zina dake kije ki fadamasa. Daman kawai sha'awarki nake amma mai zan yi dake. Kudina da kika ci kije". Wadannan sune kadan daga cikin irin kalaman da suka fito a bakin sa kenan.Sai na dauka da wasa yake yi. Amma wanka mini marin da yayi ne a lokacin da na matso kusa dashi zan rungume shi na tabbatar da gaske yake. Daga wannan marin ban ma san lokacin da ya fita ya barni kife a kan gado ba inata kuka. Ina tashi nayi kokarin kiran sa sai naga dukkannin lambobinsa ya kulleni bazan iya kiran sa ba. Haka nan na tashi na nufi gida cikin bacin rai ban iya fadawa kowa abunda ya faru ba har yau din nan.Yanzu haka a rubutun da nake yi nayi ɓatar wata, watanni biyu kenan da faruwar al'amarin kuma banga al'ada na ba. Ciki ya shiga. Ga iyayena sun matsa na ce masa ya turo. Ni kuma tun daga faruwar wannan al'amarin sonsa da kaunar sa ya kara ninka wanda nake masa a baya.Wannan yasa nace bari na kawo wannan matsalar tawa gaban dalibai domin neman shawarar abunda ya kamata nayi akan wannan matsalar da nake ciki. Na kuma jawo Hankalin yan mata Irina da suyi takatsantsa da irin mazan da suke mu'amala dasu. 


Tabbas nasan bani kadai bane da irin wannan matslar don haka yan uwa ina neman shawarar ku. Na zubar da cikin nan ne na manta dashi. Ko na bar cikin na shigar da kararsa a kotu idan yaki aurena?


Tabdi lallai kunji fa halin da wannan baiwar Allah ta shiga in akwai kaddara to kema da maki laifin. Tun lokacin da ya fara turo hotunan batsa ya kamata ki gane ba namijin kwarai bane balle har ki nemi zama inuwa da dashi a matsayin mijinki.


Mata da yawa Suna tafka babban kuskure wajen soyayya, ya manza ayi yace mako sai ya yi Zina fake zai aureki ke kuma don toshewar Basira ki yadda dagaske zai aurenkin. Kin manta da Allah shiyasa Allah Ya bashi damn cika burinsa a kanki.


Mata wannan kalubale ne a gareku. Kuma izna ne, sannan Janhankaline. Allah Ya shiga tsakanin nagari da mugu Ameen.SANARWA:


Ina meson ya mallaki website nashi na kanshi, 'yan kasuwa, da ma'aikata ga dama fa ta samu, ta hanyar tallata kasuwancinku a yanar gizo kowa yasan daku.Ina mata kuma ga dama ta samu kuzo Ku bude website dinku a kudi kalilan ki ribatu da riba mara iyaka.Shi wannan website na blogging idan ka bude shi kana rubuta labarai, ko tallata kasuwancinka KABI dokoki a karshe Google AdSense zata karbi site din ta ringa dora talla tana biyanku.Duk mai bukata ya duba contact us, akwai Email ko kuma a kira 08021045546.sai a nememu a nan sai muyi maku cikakken bayani da abinda ake biya
Sannan ba wai da min gama koya ma mutum shikenan zamu barshi ba, zamuyi ta bashi guidelines da kowane irin taimako da ya shafi blogging, har sai mun tabbatar an fara biyanshi sannan.Sai dai fa abin yana bukatar lokaci, natsuwa, karsashin da kuma juriya da hakuri. Hakuri shine jigon nasara akan komai to haka yake a harkar blogging.


Allah Ya bamu sa'a.

Comments