Main menu

Pages

YADDA DOKA KE DA TSANANI GA MASU SAFARAR SHINKAFA DA HAKA TAKE A FUSKAR TSARO DA TUNI AN WUCE WAJEN

 YADDA DOKA TAKE DA TSANANI GA MASU SAFARAR SHIN KAFA DA HAKA TAKE A FUSKAR TSARO DA TUNI AN MAGANCE MATSALAR TSARO.


Abin mamaki baya karewa a Nigeria. Yadda aka tsanantawa masu daukar shinkafa da masu daukar dai dai a mota da haka aka mai da hankali ga matsalar tsaro to da yanzu ba wannan zancen ake yi ba.
Yadda ake wulakanta masu safarar shinkafar waje, ake kwace masu dukiyoyinsu wani lokaci har a rasa rai saboda harbi da jami'an keyi  da haka ake ma masu tada kayar baya da mun huta.
Shinkafar da take a matsayin abinci amma a kasar nan an mayar da ita kamar miyagun kwayoyi. Yadda ake bincike da zuwa ana barke ma jama'a store store, ana neman shin kafa,  kamata yayi ace miyagun mutanen nan ake neman maboyansu ba maboyar shinkafa ba 

Mazaje da dama an keta masu haddi, sai tsakar dare jami'an tsaro su shigar masu cikin gida har kunyar dakin iyalansu saboda rashin sanin darajar Matan Aure da keta iyakokin  Allah. Kawai ace an zo neman shinkafa kawai don mazajensu Suna business din shinkafa.

Ace za a leka masu Karkashi gadon don neman wata banzar shinkafar da ba barazana bace a rayuwar dan Nigeria,  amma ga masu kashe kashe da satar mutane suna cin karensu ba babbaka.

Kuma a haka don an raina mana wayau ace wai gwamnatin tarayya na iya kokarinta wajen ganin an kawo karshen matsalar tsaro. A harkan???

Amma ai ta iya binciko bayin Allah da ke fadi tashin ganin sun rufa ma kansu asiri da iyakensu kawai don sun siyo shinkafar waje.
Kuma abin takaici shinkafar tamu ta gida ba a gyara ta a ingantata kamar ta wajen ba. Kun fiso talaka a kullum ya zaman cikin matsala da tashin hankali ita gwamnati ba abinda ya shafeta.

Mata da yawa sun zama zawarawa yara da yawa sun zama marayu duk din kashe masu iyaye da akai saboda safarar shinkafar waje.

Mazaje da yawa kuma an tsugunar dasu an karyasu an kwace masu jari da motar gaba daya ake kwacewa.

A yadda naji ma cewa akai duk wanda aka gani da shinkafar waje ko buhu daya ne a harbeshi. Amma ga masu ta'addanci ansa masu ido Suna abinda sukeyi.Duk wanda yake zaune a Daura to yasan fiye da abinda na rubuta. Saboda tacen ake shigo da shinkafar.
To yanzu a haka har ana da bakin gaya mana ana kokarin kan harkar tsaro.
Wallahi idan anso kafin sati an share wadannan miyagun mutanen, but anki an kyalesu.
Kwanan nan aka gano wani gida cike da bindigogi sama da dubu, harsashi sama da dubu, kayan sojoji buhu buhu. Maimakon asa zafi a tsananta bincike akan masu gidan a kamesu aji yadda suka samu wannan kayan.
A'a ba wannan ake magana ba wai sunyi laifi sun aje makamai bada izni ba. Kuma wadanda suka sace yaran makarantar jahar Naija sunce da kayan sojoji kidnerphers din suka zo. Ku duba wannan lamari fa...... Hhhmmmm


SANARWA:


Ina meson ya mallaki website nashi na kanshi, 'yan kasuwa, da ma'aikata ga dama fa ta samu, ta hanyar tallata kasuwancinku a yanar gizo kowa yasan daku.Ina mata kuma ga dama ta samu kuzo Ku bude website dinku a kudi kalilan ki ribatu da riba mara iyaka.Shi wannan website na blogging idan ka bude shi kana rubuta labarai, ko tallata kasuwancinka KABI dokoki a karshe Google AdSense zata karbi site din ta ringa dora talla tana biyanku.Duk mai bukata ya duba contact us, akwai Email ko kuma a kira 08021045546.sai a nememu a nan sai muyi maku cikakken bayani da abinda ake biya
Sannan ba wai da min gama koya ma mutum shikenan zamu barshi ba, zamuyi ta bashi guidelines da kowane irin taimako da ya shafi blogging, har sai mun tabbatar an fara biyanshi sannan.Sai dai fa abin yana bukatar lokaci, natsuwa, karsashin da kuma juriya da hakuri. Hakuri shine jigon nasara akan komai to haka yake a harkar blogging.


Allah Ya bamu sa'a.


Kai daji kasan akwai rainin wayau a al'amarin tsaron kasar nan. To mudai Allah muke roƙo da ya kawo mana dauki, Ya yi mana maganin wannan matsala ta tsaro Ya kare musulmai Ya kare yankinmu na arewa alfarmar Annabi Muhammad SAW. Ameen


.

Comments