Main menu

Pages





A yau zamuyi bayani akan yadda ale yin Dambun shinkafa, da yadda ake Alkubus na Alkama da Alkubus din flour da ydda ake vegetable soup.


DANBUN SHINKAFA

Abubuwan da za a Bukata

Shinkafa

Zogale

Mai

Tattasai

Albasa

Nama ko kifi

Maggi

Gishiri


Yadda Zaki Hada

A barzo shinkafa sai ki sa rariya tankaden gari ki fidda gari dan kar dambun ya hade. Saiki wanke shinkafar da aka barza ki yanka nama kanana cikin ta saiki juya su hade ki zuba ga a madanbaci, 



Amma idan da kid za ki amfani to sai kin yi hawa na daya, ma'ana sai kin fata turara Dambun idan za ki zagaye na biyu sai ki sauka kifin.



Saiki yanka tarugu albasa da tattasai ki hada da zogale ki wanke. Saiki kwashe danbun da kika dora a wuri mai fadi ki zuba su zogale da maggi da gishiri kiyayyafa ruwa ki juya su hade ki mayar ya qara turara idan yayi ki sauke kisa mai shikenan. 



Amma idan da steamer zakiyi komai zaki zuba a shinkafar ki zuba. Amma idan da abun yi na gargajiya zakiyi yafi kyau ayi bugu 2 yadda nayi bayani. Kuma idan kinaso zaki iya sa su karas, nidai da kifi nayi amfani aci lafia


VEGETABLE SOUP

Ugu

ganda

nama

Crayfish 

maggi

spices

manja

tafarnuwa

taruhu

tattasai

albasa.


Yadda ake hadawa


Zaki wanke ganda ki gyarata sai ta yi fari ki dafa tayi laushi ki wanke sai ki hada da nama ki dafa su da Maggi sai spices da albasa ki ajje agefe da ruwan naman.


Ki yanka ugu ki wanke tas sai ki tsane shi ki ajje agefe.


ki jajjaga taruhu alayyahu da albasa sai ki yanka wata albasar ki ajje


ki daka tafarnuwa da daddawar yarabawa sai ki ajje


ki hada kayan miyan da daddawar a tukunya kisa mai ki soyasu sai ki sa albasa su soyu tare ki zuba ruwan nama da nama da ganda sai kisa maggi spices da crayfish ki juya ki bari ta soyu sai ki zuba ugun ki juya sai ta turara ya dan dahu sai ki sauke shikenan.



ALKUBUS NA ALKAMA

KAYAN AIKI

garin alkama

Yeast 

Gishiri

Ruwan dumi yadda ake bukata

Mai

MATAKAI

Da farko zaki samu garin alkama ki zuba a roba me zurfi sai ki zuba yeast, mai babban chokali 2 da gishiri.


Sai ki rika zuba ruwan dumi kadan kadan ki kwaba da muciya ko hannu bayan kin wanke har sai ya hade amma kada yayi ruwa tsululu kuma kada yayi tauri, ki buga shi sosai sai ki sami ki rufe ki sa waje mai dumi ya tashi



Bayan ya tashi sai ki sake buga shi, sai ki shafa mai a cikin mazubin da zaki zuba ki dibi kullun ki zuzzuba a ciki amma kar ki cika saboda zai kara tashi sai ki jera cikin steamer ki rufe da buhu kar tiririn ya rika fita,


ki zuba ruwan dumi cikin kasan steamer din ki dora kan wuta, idan ruwan na kara zafi zai sa ya kara tashi kafin ya fara turaruwa



Idan ya turaru zaki ji kamshi ya cika Koina ko ki sa wuka ciki idan ta fito ba kullin a jiki alkubus dinki ya turaru. Sai ki sauke, a ci da miyar taushe mai kabewa ko farfesu



ALKUBUS NA FULAWA


KAYAN AIKI

Fulawa 

Yeast 

baking powder

Mai dan kadan

Gishiri dan kadan


Yadda za a hada

Zaki tankade fulawa ki zuba a roba sai kisa gishiri da baking powder da yeast ki jujjuya sannan kizuba mai ki sake jujjuya sai kizuba ruwa ki kwaba sosai zakiyi kwabin kamar na fanke. Idan kin kwaba sai kirufe kibarta na awa daya ko fiye da haka don yatashi



Bayan yatashi sai kidauko robar da zaki dafa da ita sannan ki shafa mai acikinsu sai ki zuzzuba aciki sannan kirufe



Sai kidaura tukunya babba a wuta sannan kizuba ruwa kadan sai ki samo wani murfin tukunyar da zai iya shiga cikin tukunyar sannan ki jejjera robobin aciki sai ki rufe kibarta ya turaru sai  kisauke idan yayi


Zaki iya hadashi da ko wane iri miyarda kikeso amma yafi shiga da miyar taushe


           

  SANARWA:


Ina meson ya mallaki website nashi na kanshi, 'yan kasuwa, da ma'aikata ga dama fa ta samu, ta hanyar tallata kasuwancinku a yanar gizo kowa yasan daku.



Ina mata kuma ga dama ta samu kuzo Ku bude website dinku a kudi kalilan ki ribatu da riba mara iyaka.



Shi wannan website na blogging idan ka bude shi kana rubuta labarai, ko tallata kasuwancinka KABI dokoki a karshe Google AdSense zata karbi site din ta ringa dora talla tana biyanku.



Duk mai bukata ya duba contact us, akwai Email ko kuma a kira 08021045546.sai a nememu a nan sai muyi maku cikakken bayani da abinda ake biya




Sannan ba wai da min gama koya ma mutum shikenan zamu barshi ba, zamuyi ta bashi guidelines da kowane irin taimako da ya shafi blogging, har sai mun tabbatar an fara biyanshi sannan.



Sai dai fa abin yana bukatar lokaci, natsuwa, karsashin da kuma juriya da hakuri. Hakuri shine jigon nasara akan komai to haka yake a harkar blogging.


Allah Ya bamu sa'a.

Comments