Main menu

Pages

 

Labarin wani Mutum da Iyalansa. Labari mai matukar ban tausayi da al'ajabi.


Assalamu Alaikum barkanmu da sake haduwa bayan dan lokacin da muka dauka baku jimu ba.



Akwai wani Mutum da yake zaune da iyalansa Matansa biyu sai 'ya'ya maza da mata. 




A cikin mazan akwai wadan da suka tasa wasu sun girma.



Wannan bawan Allah ba shi da wata sa'a sai gadi, kullum da wannan aikin gadin nasa suke ci su sha har ayi sutura.




Kuma duk da kasancewar shi mai gadi yana iya bakin kokarin sa wajen ganin ya kyautata ma iyalansa.



Duk da dan abinda ya ke samu ya sauke nauyin iyalansa, haka ya kukuta ya bude asusu YANA tara dan abinda Allah Ya hore masa.




Ya dauki lokaci mai tsawo yana tara kudi a cikin asusun nan.




Wata rana sai ya dauko asusun ya bude, ya kirga kudinsa kudi kuwa masu yawa ba laifi. 




Cikin kudin sai yaje kasuwa ya siyo masu danyen nama ya kawo gida yace a dafa kowa yaci. Saboda kyautatawa.




Sauran kudin sai ya Uwargidan sa yace ta ajiye mashi. 




Naman nan kuwa suka soyeshi, sai daya daga cikin Matan tace tunda yanzu dare yayi a bar naman nan da safe sai a raba.




Haka kuwa akayi aka dauki nama akaje aka ajiye. Dare yayi kowa yayi barci.





Sai Amaryar ta farka saboda surutun da take taji a bayan gidansu.

Sai ta tashi ta nufi dakin Uwargidan.





Tace mata niko surutu nike taji a bayan gidan nan anya ba shigo mana za ayi ba.





Uwargida tace dagaske, muje inji, suka je ta wajen dakin Amaryar sukaji surutai sosai ga dukkan alamu sun kusa haurowa.





Uwargida tace kinsan me za ayi yanzu. Amaryar tace a'a, Uwargidan tace ina naman nan yake, dauko shi kiga yadda zamuyi.





Amarya ta dauko naman nan, Uwargidan ta dauko shinkafar bera ta bade naman nan dashi suka bar shi nan falo





Barayin nan bayan sun duro suka shigo suka ci karo da nama, sukace ah lallai kuce kinsan da zuwanmu kenan tunda kuka tanadar mana wannan soye






Suka ci naman nan sosai sannan sukace a basu kudin da Maigidan ya bada ajiya.




Nan take Uwargidan ta dauko ta basu. Sun karba zasu fita mutum biyu cikinsu suka fadi nan tsakar gida suka mutu.




Sauran biyun kuma Suna fita kofar gida suma suka fadi suka mutu.




Gari na wayewa cikin gawar barayin nan akaga ashe harda Dan Amarya, shine yaje ya gayyato abokansa don azo a kwace kudin Ubansa mai gadi da yasha wahalar tarawa.





Nan take hankalin Uwargidan ya tashi matuka, tace itace sanadi. Saboda itace ta bada shawaran asa shinkafar bera a naman da sukaci.





Amarya tace haba aiun yanzu kenan yana yin jagora don azo a saci kudin Ubansa to nan gaba waya san abinda zai zama. Don haka mutuwarsa ya fiye mata kwanciyar hankali.




To Allah Ya shirya mana zuri'a ya kare mu daga sharrin shaidan Ameen.




Ku cigaba da kasancewa damu a taskarmuu don kawo maku muhimman abubuwan da suka shafi rayuwa.



SANARWA:


Ina meson ya mallaki website nashi na kanshi, 'yan kasuwa, da ma'aikata ga dama fa ta samu, ta hanyar tallata kasuwancinku a yanar gizo kowa yasan daku.



Ina mata kuma ga dama ta samu kuzo Ku bude website dinku a kudi kalilan ki ribatu da riba mara iyaka.



Shi wannan website na blogging idan ka bude shi kana rubuta labarai, ko tallata kasuwancinka KABI dokoki a karshe Google AdSense zata karbi site din ta ringa dora talla tana biyanku.



Duk mai bukata ya duba contact us, akwai Email ko kuma a kira 08021045546.sai a nememu a nan sai muyi maku cikakken bayani da abinda ake biya




Sannan ba wai da min gama koya ma mutum shikenan zamu barshi ba, zamuyi ta bashi guidelines da kowane irin taimako da ya shafi blogging, har sai mun tabbatar an fara biyanshi sannan.



Sai dai fa abin yana bukatar lokaci, natsuwa, karsashin da kuma juriya da hakuri. Hakuri shine jigon nasara akan komai to haka yake a harkar blogging.


Allah Ya bamu sa'a.

Comments