Main menu

Pages

 


 AYYUKAN DA UBANGIJI YA TSINEWA ME MAIKATASU

       

                 DARASI NA DAYA


Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jinqai_


Abinda Ake Nufi da La'ana Ko Tsinuwar Allah Shine: Ubangiji Ya Nisanta Bawansa Daga Rahamarsa Gaba Daya. Sannan A Nisantashi da Samun Darajar Rabautattu, da Samun Matsayi Na Nagartattun Bayi.



_A Takaice Abinda Ake Cewa Tsinuwa Shine Addu'ar Nisanta Bawa Daga Samun Rahamar Ubangiji Mai Rahama. Da Wannan ne Zamu Fahimci Zantukan Sahabbai da Suke Cewa: “Manzon Allah (ﷺ) Ya La'anci Kaza”. Abin Nufi Yayi Addu'ar Allah Ya Nesantashi da Rahamar Allah._



_Kamar Yanda Muka Sani Ayyukan Zunubai Sun Kasu Kashi Kashi; a Cikinsu Akwai Manya, Kuma Akwai Kanana. A Cikin Manyan Akwai Wadanda Ubangiji Ya Sanya Kaffararsu Shine a Zartarwa Wanda Ya Aulikatasu Haddi,



 Kamar Sata da Shari'a Tayi Umurni da a Yanke Hannun Wanda Yayita Matukar Abinda Ya Sata Yakai Rubu'u Dinãr.




 Da Kuma Zina da Ubangiji Ya Shar'anta Yin Bulala 'Dari GA Wanda Be Ta6a Aure ba; Wanda Ya Ta6a Aure Kuma a Jefeshi._



_Sannan Daga Cikin Manyan Zunuban Akwai Wadanda Allah, da Manzon Allah (ﷺ) Suka Tsinewa Mai Aikatasu Wanda Yin Bayaninsu Shine Manufar Wannan Rubutun. 




Insha Allah Zamu Kawosu 'Daya Bayan 'Daya Gwargwadon Abinda Allah Ya Hore Mana. Allah Ya Tsaremu Aikata Daya Daga Cikinsu Ya Bamu Lafiya Ya Kuma Bamu Ikon Bauta Masa da Lafiyar da ya Bamu._


_1. ZAGIN MAHAIFA:


عن علي بن أبي طالب رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: *”لَعَنَ اللهُ مَنْ لَعَنَ وَالِدَهُ ، وَلَعَنَ اللهُ مَنْ ذَبَحَ لِغَيْرِ اللهِ ، وَلَعَنَ اللهُ مَنْ آوَى مُحْدِثًا ، وَلَعَنَ اللهُ مَنْ غَيَّرَ مَنَارَ الْأَرْضِ“*

```{مسلم: ١٩٧٨}```


_An Kar6o Daga Aliyu bn Abi-Dalib (ra), Daga Annabi (ﷺ) Yace: “Allah Ya Tsinewa Wanda Ya Zagi Iyayensa. Allah Ya Tsinewa Wanda Yayi Yanka Don Wanin Allah. 



Kuma Allah Ya Tsinewa Wanda Ya Taimakawa Ma6arnaci. Sannan Allah Ya Tsinewa Wanda Ya Sauya Alamar Kasa (Floti, Gona)”._

```{Muslim: 1978}```


_

Kila Wani Yayi Mamakin Ya Za'ayi Mutum Ya Zagi Mahaifansa, ba Lallai Sai Mutum Ya Bude Baki Yace Dubesu Ya Qunduma Musu Zagi ba, Hadisin da Zaizo Zaiyi Bayanin Wata Hanya da Ake bi ta Zagin Iyaye ba Tare da an Farga ba._



_A Wani Hadisin Kuma da Abdullahi bn Amru Ya Ruwaito, Manzon Allah (ﷺ) Cewa Yayi:_


عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صلى الله عليه وسلم: *”إِنَّ مِنْ أَكْبَرِ الْكَبَائِرِ أَنْ يَلْعَنَ الرَّجُلُ وَالِدَيْهِ“.* قِيلَ يَا رَسُولَ اللَّهِ وَكَيْفَ يَلْعَنُ الرَّجُلُ وَالِدَيْهِ قَالَ: *”يَسُبُّ الرَّجُلُ أَبَا الرَّجُلِ، فَيَسُبُّ أَبَاهُ، وَيَسُبُّ أَمَّهُ“*

```{رواه البخاري}```


_An Kar6o Daga Abdullahi bn Amru (ra) Yace: Manzon Allah (ﷺ) Yace: “Lallai Yana Daga Cikin Mafi Girman Zunubi Mutum Ya Zagi Mahaifansa”. Sai Akace: Yaya Za'ayi Mutum Ya Zagi Mahaifansa? Sai Yace: “Mutum Ya Zagi Mahaifin Wani, Shi Kuma Wani Shima Sai Ya Rama Ya Zagi Mahaifin Wanda Ya Zagi Mahaifinsa”._

```{Bukhari Ya Ruwaitoshi}```




_2. ZAGIN SAHABBAN ANNABI (ﷺ): 

 Haka Kuma Yana Daga Cikin Nau'in Mutanen da Ubangiji Ya Tsine Musu Mai Zagin Sahabban Annabi (ﷺ),  Hadisi Ya Tabbata Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa:_


عن ابن عباس رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم: *”من سب أصحابي، فعليه لعنة الله والملائكة والناس أجمعين“*

```{الطبراني: ١/١٤٧/٣}```


_An Kar6o Daga Ibn Abbas (ra) Yace: Manzon Allah (ﷺ) Yace: “Duk Wanda Ya Zagi Sahabbai Na, La'anar Allah, da ta Mala'iku da ta Mutane Gaba Daya Ya Tabbata Akansa”._


_Har Wayau Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa:_


عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخدري قَالَ: قَالَ رَسُولُ الله ـ صلَّى الله عليه وسلَّم: *”لاَ تَسُبُّوا أَصْحَابِي؛ فَإِنَّ أَحَدَكُمْ لَوْ أَنْفَقَ مِثْلَ أُحُدٍ ذَهَبًا مَا أَدْرَكَ مُدَّ أَحَدِهِمْ وَلاَ نَصِيفَهُ“*

```{البخاري: ٣٣٩٧ ومسلم: ٤٦١١}```


_An Kar6o Daga Abi-Sa'idil Khudry (ra) Yace: Manzon Allah (ﷺ) Yace: “Kada Ku Zagi Sahabbaina, Domin da 'Dayanku Zai Ciyar da Kwatankwacin Dutsen Uhud Na Zinari, Bazai Riski Mudun Dayansu ba Ko Rabinshi_

```{Bukhari: 3397, Muslim: 4611}```



3 MAI CIN GANCI DA MAI BAYAR DASHI

: Mai Bayar da Cin Hanci Yana Mai Jin Dadi ba Tare da Tilastashi Akayi ba da Wanda Ya Kar6a Cin Hancin Suna Dãgã Cikin Jinsin Mutanen da Ubangiji Ya Tsine Musu. Manzon Allah (ﷺ)Yana Cewa a Cikin Ingantaccen Hadisinsa:_



عن عبد الله بن عمرو رضي الله عنهما قال: *”لعن رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم الراشي والمرتشي“*

```{الترمذي: ١٣٣٧}```



An Kar6o Daga Abdullahi bn Amru (ra) Yace: Manzon Allah (ﷺ) Ya Tsinewa Mai Bayar da Rashawa da Wanda Ya Kar6eta”._

```{Tirmizi: 1337}```



 YA ALLAH KA KAREMU AIKATA 'DAYA DAGA CIKIN WADANNAN AYYUKAN, KA BAMU IKON AIKATA ABINDA KA YARDA DASHI



SANARWA:


Ina meson ya mallaki website nashi na kanshi, 'yan kasuwa, da ma'aikata ga dama fa ta samu, ta hanyar tallata kasuwancinku a yanar gizo kowa yasan daku.



Ina mata kuma ga dama ta samu kuzo Ku bude website dinku a kudi kalilan ki ribatu da riba mara iyaka.



Shi wannan website na blogging idan ka bude shi kana rubuta labarai, ko tallata kasuwancinka KABI dokoki a karshe Google AdSense zata karbi site din ta ringa dora talla tana biyanku.



Duk mai bukata ya duba contact us, akwai Email ko kuma a kira 08021045546.sai a nememu a nan sai muyi maku cikakken bayani da abinda ake biya




Sannan ba wai da min gama koya ma mutum shikenan zamu barshi ba, zamuyi ta bashi guidelines da kowane irin taimako da ya shafi blogging, har sai mun tabbatar an fara biyanshi sannan.



Sai dai fa abin yana bukatar lokaci, natsuwa, karsashin da kuma juriya da hakuri. Hakuri shine jigon nasara akan komai to haka yake a harkar blogging.


Allah Ya bamu sa'a.

Comments