Main menu

Pages

YIN WANKA KULLUM MATSALANE GA FATAR JIKI...

 

YIN WANKA kullin YANA KAWO MATSALA GA JIKIN DAN ADAM – MASANA....


Masana lafiyar fata sun bayyana cewa yin wanka a kulli yana baiwa jikin ‘dan adam matsala.


DABO FM ta binciko wani bincike da Likitocin kula da lafiyar fata na duniya  suka gudanar akan illar yin wanka kullum.


Likitocin sun bayyana cewa “Illar yin wanka a kullin yafi amfanin yin wankan a kulli yaumin saboda illar da yake haifar wa fatar jikin mutum."


“Muna yin wankan da ya wuce gona da iri. Amma yana da kyau mu gane cewa muna yin hakan ne kawai saboda wasu abubuwan yau da kullin, ko kuma saboda iyaye da kafafin labarai suna fada mana haka domin tseratar da jikinmu daga yin wari.” – Dakta Ranella Hirsch.


“Sai dai gaskiyar magana, wanka sau daya a rana ma yana tsotsar da ruwan jiki tare da cire sinadaren maiko a jikinmu.”


“Jikin dan adam yana fitar da wasu sinadaran maiko wadanda suke taimakawa wajen rike ruwan jikin domin tafiyar da aikace-aikacen sassan jiki ba tare da wata tangarda ba.”


“Irin wannan sinadarin masu wanka a kullin suke rasa wa.”


“Iya adadin da mutum yake wanka, shine iya adadin asarar wasu nau’o’in kwayoyi masu amfani a jiki wanda hakan yana kai wa ga samun cutar fata.”


Dakta Elaine Larson ta Jami’ar Columbia, Dakta C Brandon Mitchell na Jami’ar George ta Washington dake kasar Amurka da sauran likitoci sun tabbatar da binciken.


Daga karshe binciken ya tabbatar da cewa yin wanka na kasa da minti 10 a duk bayan kwanaki 2 zuwa 3 shine abinda fatar ‘dan adam tafi so.


Sai dai a bangaren Dakta Mitchell, ya bayyana cewa yin wanka sau daya ko sau biyu a cikin mako shine abinda yafi dacewa ga dukkanin mutane. -Kamar yacce binciken DABO FM ta tabbatar.


Sau nawa kuke wanka a rana? Bayyana mana ra’ayinku a wajen bayyana ra’ayoyi dake kasan wannan rubutun.


Lallai kam, to yanzu zabi dai ya rage gareku, amma dai nasan wannan bincike zai karfafa ma kazamai kwarin gwiwar gujewa wanka.


To wannan bincike dai yawancin turawa ne sukayi shi, kuma kowa ya sani su ba son yin wanka suke ba, yawancin lokutta sai dai su goge jikinsa da towel.


To a kalla su zasu tsabtace jikinsa, ba zasu fito da datti ba, ba kamar mu nan ba sai kaga wani yayi wankan ma amma kamar bai yiba.


To a shawarce dai ni a ganina ya kamata ace a kalla mutum ya samu yayi wanka ko da sau daya ne a kowacce rana.


Duba da addininmu tsabta itace cikin addinin, sannan Allah Mai tsarki ne, ba Ya karbar abu sai mai tsarki. Don haka a dage da gyaran jiki da kamsasa jiki maza da mata.


Comments