Main menu

Pages

YADDA ZA A WANKE QODA (KIDNEY) A GIDA GA MASU CUTAR,

 

YADDA ZA A WANKE QODA (KIDNEY) CIKIN SAUKI BA TARE DA YIN DIALYSIS A ASIBITI BA!

A nemi Ganyen Yalo wato (Garden Egg Leaves), Sai a Dan wanke ganyen da Ruwa me kyau Sai a yayyankashi kanana-kanana, Sai a zuba a tukunya me kyau tare da ruwa me kyau.


 Sai a dora a kan wuta tsawon mintuna goma (10) sai a tace a saisai tashi kaman shayi, idan ya Dan huce Sai a shanye cikin karamin Kofi daya,

 Bayan an shanye da Dan wasu awowi in aka ji fitsari a yi a fili ta yadda za a ga kalari fitsarin ya chanza tare da fitar da wasu cututtuka daga Qoda (Kidney) Zuwa mara.


Me fama da Ciwon Qoda ya jarraba Wannan bayani Inshaa Allahu zai dace da waraka da yardar Allah! Me fama da ciwon Qoda yana iya yi kullum sau Biyu a rana har ya dace,


me son ya wanke Qodarsa kuma Sai ya dinga yi sau daya akowacce rana Na tsawon sati daya.


Yah Allah ka bamu Lafiya da zaman lafiya,AMFANIN  KARAMFANI GUDA BAKWAI (7) GA LAFIYAR DAN ADAM 


Mafi yawan Mutane Suna Kallan Kaninfarine kawai domin Sanyawa a shayi ko kayan kamshi irin na yaji da makamantan su.


Amfaninsa bai takaita iya nan kawai ba, domin yana maganin abubuwa da dama kamar;


1 ) CIWON HAKORI: dandaqashi akeyi a lika cikin hakori


2 ) *BASUR : jikashi ake ya tsumu, kullum sai asha cokali uku da safe da dare


3 ) MAGANCE MATSALAR WARIN BAKI : jikashi ake da lemon tsami da garin habbatus sauda adinga kuskure baki dashi kullum da safe da rana da dare


4 ) WANKE JINI : jikashi ake da tsamiya adinga sha sau daya Kullu


5 ) MAGANAR LARURAR SIKILA :Tafasa shi akeyi tare da Zogale adinga shan ruwan ana cinye ganye


6 KORAR MACIZAI DAGA GURI :Yadda mata Suke turaran kamshi, idan aka Dan zuba ko guda bakwai ne acikin garwashin, to macizai basu zama agurin, idan akwai suma sai sunyi kaura awajan


7 ) MAGANCE MATSALAR WAHALAR HAIHUWA : Kullum me ciki ta dinga Samun kaninfari tana taunawa kamar gudu uku tana hadiye ruwan yawun bakinta idan ta tauna


Da yardar Allah ba zatayi doguwar nakudaba ko kuma ace ta wahala wajan haihuw


Ya Allah ka cigaba da wadatamu da lafiyar Zuciya da gangar jiki gaba daya Ameen
SIRRIN FARAREN HAKORA: HANYOYI 8 DA ZA KU BI DON SANYA HAKORANKU SUNA SHEKI

- Fararen hokara na kara kwarin gwuiwar magana a cikin abokai ba tare da jin kunya ba.


- Yawancin mutane ba su da masaniyar yadda zasu magance matsalar rashin fararen hakora wasu har suna zaton halitta ne, to ga hanya mai sauki.


Kamar yadda kowane sashi na jikin dan Adam yake bukatar kulawa, haka zalika Hakora ma na bukatar kulawar mai su.


 A yau zamu bayyana hanyoyin da za a bi cikin sauki don samun lafiyayyun hakora masu haske da sheki har ma su rika walkiya.


 Hanyoyin sune kamar haka:


Dabi’ar cin abinci:

Da farko dai sun bayyana cewa dole mutum ya canja dabi’arsa ta cin abinci, ma’ana mutum ya kasance yana cin abubuwa mai gina jiki, kuma yana da kyau ya gujewa cin abincin da yake da tarin sukari a cikinsa (Sugar). 


Ta’ammali da abubuwan da suka  hada Madara, Nono da kuma shan wadaccen ruwa mai tsafta da sauransu yana inganta lafiyar Hakori.


Amfani da Danko (Chewing Gum)

Taunar Danko wato wanda aka fi sani da Chewing gum a turance yana taimakawa matuka gaya wajen hana zaman wani abu a cikin sakon hakori, 


a sanadaiyyar hakan ka iya jawo tsutsar hakori dama sauran dangogin matsalolin da suka shafi hakorin baki daya.


Amfani tare da sauya magogin baki (Toothbrush)

Yana da matukar muhimmanci, wanke baki akai-akai domin yin hakan zai taimaka wajen wanke tare da fitar da duk wani nau’in abun da ya makale a hakorin. 


Haka zalika yana da kyau ace mutum yana sauya magogin bakinsa duk tsawon wani lokaci (a kalla duk bayan wata uku). Bayan amfani da magogin baki yana da kyau ace an wanke da ruwa mai tsafta sannan a barsa ya bushe tare da samar masa wajen ajiya mai kyau,


 amma kar ya zama ana barinsa a bayan gida (Toilet) kamar yadda wasu suka maida dabi’arsu, wanda hakan ka iya jawo wasu kwayoyin cututtuka su hau kan shi magogin bakin.


Kulawa ta musamman ga hakora:

Kungiyar kula da lafiyar hakora ta duniya wato International Dental Health Association, ta bayyana cewa kaso 42% ne na mutane ke amfani da magogin baki domin kula da lafiyar hakori. Sun sake jero wasu hanyoyin da suke ganin yin su zai taimaka gaya wajen samuwar ingantattun hakora;


Wanke baki da magogi har na tsawon mintuna biyu (2 Minutes) akalla sau biyu a rana.


Kuskure baki da ruwa lokaci zuwa lokaci, musamman bayan kammala cin abinci ko wani abu mai dauke da abun da zai iya zama a hakori.


Amfani da maganin wanke baki wanda da dama daga cikinsu suna dauke da sinadarin kariya (Antibacterial) wanda yana taimakawa wajen wanke duk wani abu tare da karawa hakora kwari.


Ganin Likitan Hakori:

ziyara ga likitan Hakori yana da matukar amfani, saboda yin hakan zai taimaka wajen duba da irin halin da hakoran ke ciki, 


Sannan in har akwai wani abu da yake damun hakoran, likitan zai iya bada shawara ko magani domin kauda cutar tun kafin ta zama babba. 


Likitan zai iya yin wankin Hakori wanda hakan zai bawa mai su damar jin dadi sosai, kuma yana da kyau ake yin wanki hakori akalla sau daya a shekara.Karin amfani da sinadarin Vitamin

Kamar yadda bayanai suka gabata cewa, a kaucewa cin abubuwa masu sukari da yawa, a nan kuma an bayyana cewa amfani da abinda yake dauke da sinadarin Vitamin zai taimaka sosai. Cin abinci mai dauke da ganyayyaki kamar su kabeji, Salak, lansir,Zogale da sauran Ganye yana da amfani.


 Cin kayan itatuwa kamar lemo, Ayaba, Kankana, Inibi duk suna da fa’ida sosai wajen lafiyar hakori.


 Har wayau, cin abinda ya shafi nau’in abinda ke cikin ruwa kamar su Kifi, da sauransu wanda duk suna dauke da nau’in Vitamin D zasu taimaka gaya.


Amfani da Man Kwakwa

Mutum zai iya amfani da man kwakwa wajen wanke baki. Cokali daya na man kwakwa mutum zai diba ya wanke bakinsa har na tsawon mintuna 20 har sai yawun bakin mutum da man kwakwar sun canja launi zuwa launin madara, sannan a zubar amma fa kar a hadiye.


Mutum zai iya hada man wanke baki da kansa Makilin (toothpaste)

Akwai abubuwa da akan yi amfani da su domin hada abun wanke baki, wannan abubuwa su ne kamar haka:

Cokali 4 na hodar Calcium

Cokali 1 na Stevia

Cokali 1 na Gishiri (salt)

Cokali 2 na Baking Soda

Kaso ¼ na kofin man kwakwa

Wadannan su ne jerin hanyoyin da in kunyi amfani da su zasu taimaka wajen kara tsaftar hakori tare da kara musu inganci.

Allah Ya sa mu dace ameen

Comments