Main menu

Pages

 
🤦🏻‍♀ *NAJA'ATU* 🤦🏻‍♀ 

*WRITING BY MARYAM (MOM AFRAH)*
*DEDICATED TO MEENA ABBA*

    *GIFT FOR SIS NAJA'AT*


*INTELLIGENT WRITER'S ASSO..®📚*

{On Ward Together}
      *(GAJERAN LABARI)*
       *Page 1*
Unguwace ta masu rufin asiri dan daka kalli yanayin unguwar zaka gane ba ta masu kud'ice ba, ta masu rufin asirine  kasancewar wata yayi nisa yasa garin yin duhu gashi akwai wuta a gari ammah bako wane gidane keda fitila a kofar gidan ba wasuma gidajen ko wutar basu da ita gashi garin damina anyi ruwa sosai duk ya kwanta a wasu guraren idan harba fitala ce dakai ba sai kabi ahankali inba haka ba saidai ka jika cikin ruwa,

 wata yarinya nagani ta fito daga wani gida tana tafiya a hankali  bata wani yi nisa ba ta shiga wani gida duk a cikin layin domin baifi gida ukku neba tsakanin gidan data fito da wanda ta shiga ba Tafiya take tana kallon kasa saboda gudun kada tayi wasa santsi ya kwasheta shiyasa ta maida hankalinta ga kallon kasa ga wani irin sanyi dake ratsata dan har rawan sanyi takeyi, 

Baba ne ya taho domin rufe gidan kasancewar yau sunsha ruwa a gari bazai fita fira ba daman idan akayi ruwa da wuya su zauna majalissa ganin yarinya na niyan kai mashi karo yasanya yayi saurin  kaucewa ya bata fili tare da haskata da fitilar dake hannunshi ya  furta waye 

A tsorace ta dago danjin muryan mahaifinta wanda taga kamar a turoshi dan ita ko kadan bata ganshi ba dukda cewar shi akwai fitila hannunshi ga kuma hasken wutar dake tsakan gida dandai wutan ba karfi sosai shiya hana hasken ya gauraye ko ina na gidan 
Ke ina kikaje da wannan daran?

 baba innace ta aikeni gidan jamila na siyo mata goro

Kallonta yayi tare da cewa wuce kije ki kwanta.

   rabawa tayi ta wuce ta nufi dayan bangaran kasancewar gida kashi biyu ne gidane na masu rufin asiri bakin gwargwado kasancewar da yana dan samu sosai yanzu ne dai abin ya tsaya Amman yanzu ma Alhamdulillah tunda basu rasa naci da sha ba dana suttura harma su taimakawa wasu dashi
Naja'atu diyace ga  Alhaji Mustapha da Hajiya Sainah su hudu Allah ya basu  Salisu ne babba sai Naja sannan Sani sai Musa auta  

Alhaji Mustapha su biyu iyayensu suka haifa shine babba sai k'aninshi  Bilya mahaifinsu ya rasu shiyasa ya dauko mahaifiyarsu daga kauye ya maidota mai'aduwa suke zaune gida daya tare da iyalinshi 
Naja'atu ita kadaice 'yarsu mace shiyasa suke matukar sonta Amman sonda suke mata bai hanasu bata tarbiya mai kyau ba, ba laifi nNja nada   tarbiya daidai gwargwado saidai barta da d'an rawan kanta tare da surutu dan idan ka ganta cikin kawayenta yanda kasan aku amman cikin manya da wuya kaji duriyanta ko babba na magana kaji bakinta a ciki mutukar bada ita yake maganarba

Kasancewarta mace itace ke taya inna kwana komai nata ma achan  yake  sosai inna ke nuna mata gata bata son abinda zai taba mata ita saboda sunan mamarta gareta kunsan mutanan da suna mutunta masu sunan iyayensu suna basu daraja da wuya kuji ko sunansu sun kira

Tunda inna tayiwa baba magana tace su uwata ankusa gama karatun nasara sai amre kuma ko?

 baba yace a'ah inna ai wata makarantar zatayi basu gama ba tukun.

 tofa tunda inna taji wannan maganar hankali yaki kwanciya kullum cikin tsegumi take wai yarinya saita girme za'ayi mata aure diya ta isa aure ace zata wani yi karatu saita girme anrasa mai sonta ita gaskiya bata yarda ba dole a aurar da ita mu namu lokaci ina muka kai kamarta ba aure kaima kasan da ace a kauye take bazata wuce haka ba babu aure ga sa'anninta nan duk za'a aurar dasu bana so kake abar maka ita tayi ta zama hakaKullum inna bata da magana saina a aurar da Naja'atu da wuya baba yazo gaishe da ita bata yi mashi wannan maganar ba yarinyar dako primary bata gama ba dan yanzu primary 6 take dandai tana da dan jikin girma.


 yanzu ma hakance ta kasance babane ya dukar dakai kasa inna sai fada take yarinya ta fara girmewa ankiyi mata aure ace har tak'ara yin wata makarantar nan gaba kamin ayi mata aure kamar ita duniyar take jira wannan ma maganar banza ce.


Inna kiyi hakuri dan Allah ki daina daga hankalinki akan wannan maganar Naja'atu fa karamar yarinya ce domin mu anan ko tankawar saurayi bata isa ba bare harya biyota yace tanaso saboda tayi kankanta

Hannu ta shiga tabawa tana salata kai kace wani babban abu ya faru  lallai Mustapha ni zaka kalla kace man Naja'atu yarinya ce ko tankawar saurayi bata isa ba? a'ah yanzu aka haifeta karewa,  so kake sai yarinya ta zama sa'ar mahaifiyanta sannan kace ta isa aure to bari kaji indai harka barta ta tsofe bamai ganinta yace yana sontaInna kiyi hakuri insha    Allah bazata dade sosai ba tunda bakiso Amman zataci gaba da karatu har Allah yasa ta samu mijin saboda yanzu ita bata da wani wanda yace yana sonta

Yauwa dan albarka haka zakace ta fada tana mai yin murmushi fadada murmushinta tayi tare da cewa to kodai kauye zamu bincika ayi mata auran gida


Baba ne yace haba inna kodai neman kai kike da maman taki dadai kinyi hakuri idan Allah yasa ta samu wani anan din sai ayi mata 

To shikenan tunda haka kace Allah bata na gari amin tace tare da mikewa yace na barki lafiya
Alhaji Mustapha yana da buri sosai akan yaranshi suyi karatun boko saboda ganin amfaninshi da yake yi ga mutane shiyasa har Naja'atu yaso tayi secondary harta shiga makarantar lafiya watau Health  Amman ba yadda ya iya saboda mahaifiyarshi ta sanyoshi gaba akan kada Naja'atu tacigaba da karatu shiyasa ya fidda ran zatayi karatu mai zurfi ya san saiya dage sosai inna zata bari ko S.S.C.E tayi dan yasan ba karamar fama zaiyi da ita ba akan hakan duk da ya san da wuya yanzu a karanci shekaru irin na Naja'atu wani ya ganta yace yana sonta tunda nan ba kamar kauye neba akwai wayewar zamani

Share

&

*Comment**MUMMYN AFRAH✍*

Comments