Innalillahi Wa inna ilaihi raajiun!!!
JAMA'A AKWAI KALUBALE BABBA DUBA DA WANNAN ZANCE....
Imamu kurdubi yace:-
An Tambayi Wani Babban Malami Mai Suna Ibrahim Ibn Adhama. "Mai Yasa Muke Addu'a Ba a karba mana?Sai Yace;-
Zuciyarku Ta Mutu Akan Abubuwa Guda 10.
(1)Kunsan ALLAH Amma Baku Bashi Hakkinsa ba.
(2)Kunsan Aljannah Amma Baku Nemeta Ba.
(3)Kunsan Wuta Amma Baku Gujemata ba.
(4)Kunsan Mutuwa Amma Bakuyi Mata Tanadi Ba.
(5)Kunsan Kur'ani Amma Kunki Aiki Da Shi.
(6)Kunce Kuna Gaba Da Shaidan Amma Kuna Binsa.
(7)Kuna Binne Matattunku Amma Bakwa Lura.
(8)Kuna Cin Arzikin ALLAH Amma Bakwa Godiya.
(9)Kuna Kallon Aibin Wasu Kunbar Naku.
(10)Kuna Kurin Son Mazon ALLAH Amma Kunbar Sunnar Sa.
YA UBANGIJI KABAMU IKON KYAUTATA AYUKAN MU DA RAYUWAR MU YADDA KAKESO KODA RAYUWAR MU BA TA SO
MAGANIN KOWANE IRIN CIWO DAGA FIYAYYEN HALITTA ANNABI MUHAMMAD SAW
Wani mutun yazo gurin manzon Allah (SAW) yace ya manzon Allah banida lfy wane magani xansha inwarke?
Sai manzon Allah (SAW) yace kaje kasamu ZAMZAM ka karanta suratul fatiha kaita maimaitawa dayawa har'iya inda kake iyawa saika tofa sannan kasha kuma kashafa a inda yakema ciwo insha Allahu xaka warke..
kayi kokari idan kagani katurama wani yagani domin Al'umma su amfana,ya Allah duk wanda yatura wannan saqon Allah kabiya masa bukatarsa Allah kayaye mashi damuwarshi albarkacin annabi Muhammad (SAW)Ameeen..
WARAKA DAGA ALQUR'ANI
( HEALING FROM THE QUR'AN_)
**************
Akwai waraka mai yawa cikin Alqur'ani mai girma. Musamman akan jinyoyin da maganinsu ke gagarar likitoci.
( *_There are lots of healing from the Noble Qur'an. Especially with regards to those ailments whose cure baffles doctors._*)
Misali duk kalar jinyar ko larurar dake tare dakai ko wani dan uwanka, ka wani daga cikin muminai, ka nemi ruwan zamzam mai kyau, ko ruwan sama ka tofa wadannan addu'o'in :
( *_For example, whatever the type of ailment or distress that plagues you or any of your relations, or anyone from among the believers, just get Zamzam water that is good or rain water, and recite the following over it:_* )
1. Fatiha kafa 7.
2. Ayatul kursiyyi 3.
3. Ayoyi 3 na karshen suratul baqarah.
4. Suratul Ikhlas (wato Qul Huwal Lahu) kafa 11 kowacce tare da bismillah.
5. Suratul Falaq kafa 3.
6. Suratun Nas kafa 3.
7. Allahumma Rabban nas, Azhibil ba'asa washfi antash Shaafee, Laa shifa'a illa shifa'uka. Shifa'an la yughadiru Saqman (Qafa uku).
8. Ayatush shifa'i din nan guda shida (idan baka dasu to suratul Ikhlas din ta wadatar).
9. Salati ga Manzon Rahama ﷺ.
[ *_1. Surah Al-Fatiha - 7 times_*
*_2. Ayaatul Kursiyy -3ce_*
*_3. The 3 verses at the end of Surah Al-Baqara._*
*_4. Surah Al-Ikhlas (i.e. Qul HuwAllaahu Ahad) - 11 times, each complete with BismiLlaah._*
*_5. Surah Al-Falaq - 3ce._*
*_6. Surah An-Nas - 3ce._*
*_7. Allahumma Rabban nas, Azhibil ba'asa washfi antash Shaafee, Laa shifa'a illa shifa'uka. Shifa'an la yughadiru Saqman (thrice)._*
*_8. Ayatush Shifa'i, the whole six of them (if you don't have them, the Surah Al-Ikhlas above will suffice)._*
*_9. Salaatul Nabiyy ﷺ._*]
Sai marar lafiyan ya rika shan wannan ruwan tofin kamar sau uku arana, sannna ya rika shafe jikinsa dashi sau biyu safe da yamma.
( *_The ill person will drink from this water about thrice daily, and will also rub the whole body with it twice daily, morning and evening._*)
Aci gaba da yin haka har makonni biyu ko uku ko fiye da haka har sai lafiya ta samu. Ko sihiri ko shafar Aljanu, ko wacce irin jinya ce, In sha Allahu za'a dace. Domin Alqur'ani waraka ne daga kowacce irin chuta.
( *_The ill person will continue this for two weeks or three, or more, until health is fully regained. Whether it is magic or jinn attack, whatever kind of ailment it is, in shaa Allaah this will suffice. For, the Qur’aan is a healing from any kind of disease._*)
Duk da cewa Alqur'ani waraka ne daga kowacce chuta, amma fa ana samun lafiya dashi ne bisa gwargwadon imani ko yaqeenin mai yin tofin da kuma shi majinyacin.
( *_Despite the fact that the Qur’aan is a healing from every disease, health is achieved through it only in proportion to the belief or certainty of the one reciting the Qur’aan over water and the ill person._*)
Allah yasa adace.
( *_May Allaah grant success._*)
Wanda ya samu ya tayamu wajen ya'dawa ga sauran 'yan uwa musulmai ta hanyar sharing ko bugawa akan takarda araba a masallatai ko makarantu ba tare da chanza komai acikin rubutun ba.
( *_Whoever gets this should help us spread it to fellow Muslims through sharing or printing and distributing at mosques or schools, without changing anything from the writeup._*)
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
*_■This is an English translation from the original which is in Hausa. The original was written by our Sheikh, Muhammad An-Nasir Muhammad, of ZAUREN FIQHU (07064213990). This translation has been authenticated by him.■_*
MAA SHAA ALLAAH. LAA QUWWATA ILLAA BILLAAH.
Comments
Post a Comment