Main menu

PagesMe ake nufi da computer a Hausance.

Computer a Hausa na nufin na'ura mai kwakwalwa, wasu na fassarata da na'ura mai aiki da wutar lantarki ko battery. 

 Computer na taka muhimmiyar rawa a fannin rayuwar dan-Adam, wajen sauka abubuwa, sannan ana amfani da ita a office ko kasuwa ko kamfanoni. Dalilin haka yasa komai make samun sauki wajen aikisa, wajen tura sako, ko karbar sako, ko ajiye muhimman bayanai ta kowacce fuska.  

 

 Sannan computer na da sassa har guda biyu. 

1. Akwai bangaren gangan jiki wanda ale cena "Hardware" a turance.

2. Sai kuma bangaren abubuwanda ke cikin computer, wadanda ba a iya tabasu. Ana ce masu "Software"

  1. Hardware  computer; wannan bangaren kamar yadda mukai bayani ya shafi dukkan wani abu na computer misali;


Keyboards

Mouse

Printer 

CPU

Monitor screens

2. Software computer; wannan kuma ya shafi dukkan wani abin da computer ke kunshe dashi. Misali;

Window

Software Apps

Start menu da duk wasu abubuwa da aka ajiye a ciki.

Wannan shine bayanain ma'anar computer a takaice, insha Allah next time zamu shiga cikin computer sosai don koyar daku yadda zakuyi amfani da ita a saukake. 

Zamu fara daga keyboard da amfani su da yadda ake kunna computer da yadda ale kasheta ba wai any how ba.

Ku cigaba da bibiyar taskarmu don amfanuwa da abubuwan da zamu ringa kawo maku.
Comments