Main menu

Pages❗MUTUWA DOLE❗


  Yayin da ranka yazo makogoro, a wannan lokacin zaka manta da makusantanka, iyalanka ko 'Ya'Yanka balle makobta.


 A wannan lokacinne Dan Adam yakanji Qishirwa mai tsanani wacce sai ya gwammaci inama yabayar da dukkan abunda ya mallaka domin abashi ruwan koda kurbi guda ne!!.😭


ZAFINDA BAWA YAKEJI YAYIN FITAN RAI...


Hakika Fitan Rai yanada wani irin Radadi wanda babu mai saninsa saidai mamacin..😭


 mamaci yayinda Ransa yakusa fita, muryansa takan karye, karfin jikinsa yakan tafi, babu damar Ihu ko kururuwar zafin da yakeji, domin zafin mutuwa yariga ya ratsa dukkan sassan jikinsa..😭


Bazai samu daman neman taimako ba, ballantana a dauke masa zafin radadin da yakeji, sai yayi fatan wannan nishin da yakeyi ko zaizama dalilin samun rangwame amma inaa.!!😭


Idan har akwai ragowar wani Qarfi a gareshi shine za'a rinka jin wani gurnani yana fitowa daga chan chikin Qirjinsa da makogoransa yayinda rai yazo fita..Alhali launin fiskansa ya chanza saboda tsananin halin da yake cikiii!!.😭


A wannan lokacin Duniya da dukkan abin cikinta zasu zamanto ba komaiba agunsa, Ballatana Dukiya ko Mulki ko wani Gata a wannan lokacin 'Dan Adam zai gane cewa ashe shi ba komai bane... kuma tundaga sannan zai fara nadamar lokutan rayuwarsa da suka tafi awajen sa'bon Allah!!.😭


        zan mutu

        zaka mutu

        zaki mutu

wlh watarana za'a wayi gari babu mu, 

wannan Duniyar da muke nema,

wannan Duniyar da mukewa ado,

wannan Duniyar da muke takama da ita,

wallahi ba matabbata bace,,😭


wata rana zamu tattaru a gaban mahaliccin mu domin auna ayyukan mu, Allah ka gafarta mana badon Halinmu Ba..

       


YA ALLAH KAGAFAR TAMANA ZUNUBANMU.


 YADDA JIKIN DAN ADAM YAKE KOMAWA BAYAN SHIGARSA KABARI!!


{1}. A Rana ta FARKO da Gawar Dan-Adam ta Shiga Kabari, Ciki Yake Fara Wari Da Kuma Al'aura (Wadanda Dan-Adam

yafi baiwa muhimmanci kenan a rayuwa, Har ake sabawa Allah (s.w.t) saboda su.


{2}. Rana ta BIYU Jiki zai Fara Kumbura Musamman Fuska Da 'Yan Yatsu, Sai Fata ta Canza launi  izuwa koriya.


{3}. Rana ta UKU Kuma Sai Kayan Ciki Sufara Kumbura Musamman.


- Hanta.

- Qoda.

- Huhu.


Suna Fitar Da Wari Mara Dadi Wanda Hakan Zai Janyo Hankalin Kudaje Daga Nisan Kilomita Biyar.


Bayan Wadansu WATANNI Sai Tsutsa Tarufe Jiki Gaba Dayansa Tanacin Naman Jiki Har Yaqare.


Bayan Wata SHIDA Da Za'a Bude Kabari Babu Abinda Za'a gani Sai Qashin Jikin Mutum Kawai.


Bayan SHEKARA DAYA, kuwa Komai Ya Qare Sai Guntun Qashin Da Ake Kira (Ajbu-Zhanab).


Wanda Manzon Allah(S.A.W) Yafada Mana Cewa:


"Akansa Ake Kara Dawo Da Halittar Dan-Adam.


INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!


Wannan Shine Jikin Da Muka Fifita Akan Komai a Duniya! Muka Yadda Musa6awa Allah Don Gyarashi Dayi Masa Kwalliya!.


Allah kasa mucika da Imani.


Dan Allah mudinga sharing dinsa domin 'yan uwanmu su amfana

Ku karanta wannan adduar sai kuma Ku turawa Yan Uwa musulmai: ((Allahuma ya farijal hammi Waya kashifal ghammi farrij hammi wayassir amri warham du'ufi waqillata hilaty warzuqni min haisu la ahtasibu ya rabbal alameen))


 ( Annabi S A W yace wanda ya sanar da wani wannan adduan Allah Zai yaye Masa damuwansa.🍌GARABASA GUDA BIYAR GA DUK

WANI MU'MINI🍌


1. Ko kasan cewa yayin idar da kiran Sallah karka haramtawa kanka Addu'ah, domin Addu'ah a wannan lokaci ba'a juyata.


2. Ko kasan ina ake sanya zunuban

ka yayin da kake sallah?

Manzon Allah (saw) ya ce:- "Duk

lokacin da bawa ya ke Sallah ana

sanya dukkan zunuban sa a wuyan

sa da kafadun sa, duk lokacin da ya yi

ruku'u ko sujada zunuban sa za su dinga fadowa kamar yadda ganye yake fadowa daga bishiya ." 

Yakai wanda kake gaggawa ya yin ruku'u ko sujada, ka tsawaita sujada da ruku'u domin zunuban ka su ragu kada ka bari wannan garabasa ta wuce ka.


3. Ko kasan wata salihar mace ta

rasu, duk lokacin da 'yan uwanta suka ziyarci kabarin ta sai suji kamshi yana tashi, sai suka tambayi mijinta sai ya ce ta kasance tana karanta Suratul

Mulk kowane dare kafin tayi bacci.


4. Ko kasan karanta Ayatul

Kursiyyu bayan kowace sallah zaka

wayi gari tsakanin ka da Aljannah

mutuwace kadai?


5. Ko kasan idan ka idar da sallah kar kayi gaggawar tashi, domin mala'iku suna roka maka gafara.


👆Ya Allah ka sanya wannan tunatarwa ta zama SADAKATUL JARIYA a gareni da Iyayena da duk wanda ya taimaka wajan yadawa,


Amin.

Comments