Main menu

Pages

DA SA HANNUN KOWA MUTUWAR AURE A YAU..DA SA HANNUN KOWA : MUTUWAR AURE A YAU


Zaben Mace Ta Gari

A kullum ana fara ambaton a zaɓi mace ta gari a farko saboda muhimmancin mace a cikin al’umma.Kowanne namiji yana fatan ya sama wa ‘ya’yansa uwa ta gari ko da kuwa shi ya san halinsa yana da naƙasu.

 

Ya yin kuwa zaɓen mace ana son a samo ta gari duk lokacin kuwa da aka sami akasin haka shi ke haifar da matsala ko bayan an yi auren.Wasu za su iya cewa to me yasa matsalar ba ta hana auren ba?Haka ne to amma me yasa matsalar ba ta hana auren mutuwa ba?


Dalilin da yasa hakan shi ne ƙaddara da kuma rufewar ido a soyayya ko kuma girman wani ko wata makusanci ko wanda ya yi dalilin auren. Amma daga lokacin da zama ya yi zama sai a fara tunanin neman mafita. Ta yaya maza za su gane mace ta gari?


Mace ta gari ita ce ta siffantu da kakkyawar ɗabi’a da halaye da kamala kallo ɗaya za a iya gane tarbiyyarta da ƙoƙarin da iyayenta suka yi wajen ba ta tarbiyya.


Mace ta kwarai ita ce wadda kowanne namiji mai hankali zai yi fatan a ce tana gidansa ta zame masa sanyin idaniya ta zama al-mar’atissaliha da Annabi Muhammad (SAW) yace ta fi duniya da duk abin da yake cikinta.Mace ingantacciya ita ce dai matar da kowanne namiji zai so ya sami zuriya da ita.


Aure da dama a yau yana mutuwa amma sai a rasa dalilin mutuwarsa a yi ta ɗorawa wani ɓangare na daban wanda wannan kuskure ne babba.


Abinda ya kamata a lura da shi shi ne in an bi ta ɓarawo sai a bi ta ma bi sawu .


Maza suna da nasu naƙasun da rashin haƙuri amma kuma matan ma akwai gyara a yadda suke gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum a wani lokacin yana saɓawa tarbiyyarmu ta Hausa/Fulani yana saɓawa al’adunmu da addininmu.


Bahaushe tun tasowarsa yana da tarbiyya da tsari managarci don yi wa ‘ya’yansa tsani na samar da al’umma nagarta. Daga cikin abubuwan da mace ya kamata ta zama don kama hanyar mace ta gari akwai:-


Kamilalliya

Mace kamilalliya it ace wadda take me kamun kai ba ta shiga hayaniya zaka same ta ko da cikin ‘yan’uwanta mat aba ta da rawar kai bare a gun maza. Kamilalliyar mace zaka same ta ba ta da shigewa maza ko da muharramanta ne kullum in ka ganta da namiji da ya zama dole sai an gansu saboda alaƙar karatu ko aiki ko wata hujja ta daban z aka ganta a tsorace tana kaffa-kaffa.


In kuma ta sami wanda take so yana cikin matakin farko da mace ya kamata ta fara nunawa a gun duk wanda take so su ƙulla mu’amala take fatan ɗorewarta zuwa aure. Hanyoyi da dama ya kamata mace ta bi don tabbatar da cewa ita mai kamun kai ce.


Mata a yau a tunaninsu na yaudarasu don yadda suke ganin maza na haba-haba da mata ba tare da nuna wani zaɓe ba to su sani iyakar ta waje ne amma matar ta aure mai kamun kai ake nema.


Sutura

Sutura ita ce abin da ka sanya a jiki don kare tsiraici.Abu na farko da kan ja hankalin namiji ga mace har ya gane ajin da zai ajiye ta shi ne irin suturar da ta saka jikinta

Mata a yau suna tunanin bayyana tsiraicinsu shi ne hanyar da za su iya janyo hankalin namiji gare su har ya gane kyan wani bangare na jikinsu da zai kai su ga aure. 


Ko kuma wata wayewa ce da ci gaba saka matsattun kaya.Wannan babban kuskure ne namjin da wannan zai ɗauki hankalinsa har ya yi tunanin ku yi sabo to tabbas sai dai soyayya wanda a ƙarshe da-na-sani ne zai biyo bayan haɗuwar. Macen da ke sanye da suturar mutunci ake nema a aura ba ballagaza da ta gama nuna kanta a titi ba.


Surutu

Surutu barkatai alamu ne na rashin kamun kai macen kwarai ba a santa da ɗaga harshe ba ko da a cikin ‘yan’uwanta mata ne bare kuma maza. Wata matar tana tunanin in ta shiga dandazon maza ta ɗaga muryarta da zaƙewa shi ne zai janyo hankalin namiji kan ta.


Mace mai kamewa da ƙarancin Magana tana da tasiri kwarai a lokacin da ake batun aure da ma bayan an yi auren. Sau tari matsalar da ake samu na shigar aikin assha tsakanin abokin miji ko kuma wani ɗan’uwan mijin tana fara ƙulluwa ne ta yadda mace take sakin jiki ta yi ta surutu daga nan sai a gane ba ta da tsada da an yi mata ƙaramar Magana za ta faɗa.


Kunya

Kunya na da matuƙar tasiri a rayuwar yau da kullum. Mace da kunya da kara da kawaici aka santa. Bahaushe baya son mace marar kunya don haka yake tarbiyyantar da ‘ya’yansa kunya tun suna ƙanana. 


Mace marar kunya ba ta farin jini wajen al’ummar da suke da mutunci hatta a gidan aure in har yarinya ta zama marar kunya ba a taɓa samun jituwa da iyayen miji ko danginsa. A kwai alamomi da suke nuna lallai wannan tana da kunya ciki akwai:-


Ciye-ciye /Tauna

Mata a yau sun zubar da kyakkawar al’adar nan ta kame kai wajen ciye-ciye a kan hanya ko gaban samari. Mace mai ciyeciye da rashin kimtsi ko ga sa’anninta mata ba ta farin jinni bare maza. Ko kuma ta yi ta taunar cingam duk wannan alamun rashin kunya ne.


Roƙo

Roƙo shi ma wata hanya ce ta nuna rashin kunya da mata kan ɗauka hanya wayewa. Duk matar da ta fiye roko da ba ni ba ni tana kasha wa kanta wata daraja ne ga mai sonta kuma in har mace ta fiye roko to fa tana nunawa wannan da zai aure ta irin zaman da za su yi.


Hali na farko da za su sa a ran su in har suka kai ki gidansu ba za ki iya hakuri da samu da rashi ba sannan duk randa babu ba za ki iya rufa wa zamantakewar asiri ba. Roƙo ga mace babbar hanya ce ta zubar da mutunci.


Kallo

A kallo kadai ana iya gane mace mai kunya da rashinta. Yadda mace za ta kafe namiji da ido yana nuna kunyarta da rashinta musamman idan yana wata Magana. Mace an fi sanin ta da risnawa.


Rashin jan aji

Mace ta kirki da jan aji da kamewa aka santa. Kar ki zama mai girman kai amma ki zama kin san darajar kanki. In har za ki zama arha kowanne namiji ya kira ki ba tantancewa ki je kowa yake bukatar jin hira da yawo ke za a zo nema a tafi da an ce ana sonki to fa ke kasuwa ta bude ba sauran excuse to fa kin kaɗe ba ki sa ɗan-ba ba a wajen neman mijin aure ba ko da kuwa rabon ya rantse an yi auren to da wuya auren ya kai labari don ko bayan kina gidan mijin zai ke zargi da tunanin halinki na rashin aji.


Makauniyar soyayya


A duk lokacin da zafin soyayya ya ja ki ko dai ke don son da ki ke yi wa mijin ko don shi son da yake ikrarin yana yi miki ko ma don a tunaninki mallaka masa kan ki da ki ka yi shi ne matakin farko na wajibcin sai ya aureki to kin yi kuskure.


Maza ƙalilan ke iya wannan halascin ga mata. Wasu matan ana yaudarar su ta hanyar kai kuɗin aure gidansu da an kai sai iyaye su aminta da wanda ya kai kuɗin su sallama masa yarinya ita kuma sai ta saki jiki wanda aure da dama da abin nema ya samu sai aure ya fara rawa Kenan kuma ko da an yi auren wannan abinda ki ka yi sai a ƙarshe in aka yi rashin sa’a ya janyo matsala duk kuwa da shi ne ma ya janyo hakan ta faru shi ya yaudare ki ya yi miki romon baka.


In kuwa haka ne to da sa hannun mata a yau wajen mutuwar aurensu don duk auren da ba a yi masa ginshiƙi na kwarai ba na matar da za a aura akwai yiwu war mutuwarsa.


Allah ya nuna mana mako na gaba inda za mu kalli ɓangaren maza su ma mu ga ta ina suka sa hannu a mutuwar aure a yau.


Quoted from

*Islamic medical center*

Comments