Main menu

Pages

ANA NEMAN TASHAR AREWA24 DA SU TAIMAKI JARUMI ALH BUBA NA DADIN KOWA.

 Matsalar Dake damun Alh Buba na dadin kowa, ana Neman a taimaka masa ya samu lafiya.

Kowane mutum akwai ƙaddararsa a rayuwa, ga duk mai kallon shirin DADIN KOWA na tashar AREWA24 ya san Alhaji Buba mai kuɗin Dadin Kowa.


Na tabbatar duk wanda ya ga wannan hoton ba ya bukatar ƙarin bayani zai gane cewa ba shi da lafiya.


Tun kafin lalurar ta yi tsanani na ja hankalin wasu daga cikin ma'aikatan shirin da su yi magana da gidan Talabijin ɗin a taimaka masa da magani domin samun waraka.


Ban san yaya tsarin gidan Talabijin ɗin ya ke ba, amma a tunani na ya dace a tallafa masa musamman ya bayar da lokacin sa na tsawon shekaru yana aiki tare da su.


Zuwa yanzu ciwo ya kai ciwo dole sai da aka cire shi daga wannan shiri aka kawo madadinsa. 


A bincike na an tabbatar min cewa, haɗakar jaruman shirin sun yi kokarin haɗa wani abu sun ba shi, ban san ita AREWA 24 ɗin ba.


Kira na a nan idan akwai yadda za a iya ceto rayuwar sa ko ba shi wani agaji a taimaka a kula da lafiyar sa, ya zama abin tausayi.

Comments