Main menu

Pages

YANDA ZA AYI AMFANI DA GANYEN GWABA WAJEN MAGANCE CUTUKA

 



Cutuka guda bakwai (7) da za a iya amfani da ganyen Gwaba wajen magancesu.

Ganyen Gwaiba ya kunshi tarin sunadarai da masu yakar cututtuka iri-iri tare da inganta lafiya musamman a yayin da aka sarrafa kuma aka yi amfani da shi ta hanyoyin da suka dace.



Ganyen dan itaciyar yana dauke da wasu muhimman sunadarai masu zaman maganin cututtuka musamman wadanda aka sani a wannan zamani.



Daga cikin sunadaran da ganyen gwaiba ya kunsa akwai; antioxidants, antibacterial da anti-inflammatory irin su polyphenols, carotenoids, flavonoids da kuma tannins dake da matukar bayar da tallafi wajen kawar da wasu cututtuka da dama.



Tasirai da wannan sunadarai suka kunsa tare da rawar da suke takawa wajen kiwatar lafiya sun hadar da;


1. Rage nauyin jiki

2. Tasiri ga cutar ciwon suga (diabetes)

3. Rage teba da daskararren maiko (Cholesterol)

4. Tsayar da amai da gudawa

5. Hana kamuwa da cutar nan ta huhu da ake kira Bronchitis.

6. Waraka ga cututtukan hakori, makoshi da kuma dadashi.

7. Ciwon daji wato Kansa.

Allah Ya sa mu dace da dukkan Alkhairai

Comments