Main menu

Pages

YADDA YA KAMATA MACE TA KULA DA KANTA LOKACIN AL'ADAH

 



Yadda Mace zata kula da kame jikinta a duk lokacin da takeyi Al'adah.

 Lokacin al'ada, lokaci ne da mace zata tsaya ta kula ta ga cewa bata sakin jikinta kamar lokacin da bata al'ada, musamman ma BUDURWA wacce bata taba aure ba, har itama matar auren wacce ta san ciwon kanta, kuma ba ta son ta ga miji yayi watsi da ita da wuri ko yana tunanin Karin aure da wuri, to sai ki tsaya ki maida hankali wajen kulawa da jikinki a lokacin al'ada da kuma haihuwa.




 Saboda ita mace a duk lokacin da take cikin al'ada to a wannan lokacin jikinta budewa yake yi, shi yasa idan mace na cikin al'ada idan akwai iyaye a kusa, sai su rinka hanata daukan abu mai nauyi, kamar bokiti dake cike da ruwa, ko tsalle - tsalle da abubuwa da na rashin kame jiki. Saboda a wanna lokacin jikinta a bude yake.



 Idan ko tana wannan kazar-kazar din to dukkanin jikinta budewa yake yi.


 Don haka idan budurwa tayi aure kuma ta kasance mai irin wannan dabi'a shine sai ki ga an sami matsala da mijinta yana zarginta da ko tana yawon banza tunda bai sameta a matsayin wacce bata taba aure ba.



    Nan kuwa ba haka bane, rashin kame jiki ne ya jawo a yayin al'ada.

 Idan kuma matar aure ce to sai ka ga jikinta ya sake budewa, idan ta gama al'ada ta koma turaka sai ki samu maigida bai damu da ya rinka waiwayarta ba saboda a madadin jikinta ya matse, a a sai ma Kara budewa da yayi.


    


  Don haka idan har kina cikin al'ada ya kamata ki kula da irin zaman da Zaki da tafiya ki kuma kiyaye da daukan Abu mai nauyi.

Comments