Main menu

Pages

AMFANIN BAWON ALBASA GUDA BAKWAI (7) GA LAFIYAR JIKIN DAN ADAM

 Amfanin Bawon Albasa guda (7) ga Lafiyar Dan Adam, da ya kamata Uwargida da Amarya masu zubar da Bawon Albasa su sani.


Amarya uwargida Daga yau kada kisake jefarda  bawon albasa..

 Bawon albasa yanada amfani matuka ajikin mutum, shikadai yana kunsheda sinadarai masu fada da cututtuka ajiki.
Idan aka samu bawon albasa aka wankeshi sosai dattin yafita sai a zuba shi acikin tafasasshen ruwa abarshi yajika daga bisani sai asha kofi daya dasafe kofi daya dayamma wannan zai taimaka wajen:- Rage kiba.

- Yana magance ciwon mara lokacin al'ada na mata.

- Yana magance rashin bacci ko karancinsa.

-Yana magance hawan jini.

- Yana magance ciwon hakori ko dadashi idan ana kurkure baki dashi.

- Yana magance matsalan yankewar numfashi.

- yana magance matsalan dandruff ko tsinkewar gashi idan aka wanke gashin dashi kafin ashiga ayi wanka.
Amfanin bai tsaya dagananba wannan dan kadan muka kawo,

Idan ana biye da wannan shafi watarana zamu kawo sauran amfaninsa Insha Allah


A turawa yan uwa su amfana

Comments