Main menu

Pages

AMFANIN AYA GUDA BIYAR GA LAFIYAR JIKI DA MASANA SUKA BINCIKO

 



Amfanin da Aya ke dashi guda biyar ga Lafiyar Dan Adam.

Aya tana da matukar amfani sosai kama tun daga ganyenta, saiwarta, da 'ya'yanta. Ga kadan daga cikin amfanin aya ga lafiyar jikinmu.




1.  Aya Na Gina Jiki Cikin Gaggawa.

Sanin sirrin da ke tattare da aya da masana ke da shi sakamakon zuzzurfan bincike da aka gudanar kanta, ya sanya ake amfani da aya wajen gina jiki. Wannan dalili ya sa ake amfani da aya a yankunan dake fama da karancin abinci mai gina jiki. Ana amfani da aya wajen inganta kiwon lafiya ga ma su fama da karancin abinci mai gina jiki sakamakon yawan sanadarai ma su matukar amfani ga jiki da aya ke kunshe da su, kamar sinadaran carbohydrate, magnesium, phosphorus, iron, fiber, calcium, sodium, copper da kuma zinc.




2.  Maganin Matsalolin Ciki.

Aya na da matukar fa'ida wajen maganin matsaloli da kan shafi ciki. Ba don komai aya ke taka wannan muhimmiyar rawa kan matsalolin ciki ba, sai dai sakamakon wasu sinadarai da ta ke dauke da su, dake inganta wa tare da magance matsalolin ciki musamman wadanda su ka shafi hanji. Sakamakon haka ta ke taimakawa wajen maganin cushewa da kumburin ciki.





3.  Gyaran Jiki.

A nan idan ana maganar gyaran jiki mu na nufin inganta lafiyar jiki da suka hada da gyaran fata, gudanuwar jini, kuzarin jiki da sauran su. Yawan sanadaran gina jiki da aya ke da su ya sa ake amfani da ita wajen gyaran jiki, sakamakon haka ta ke gyara fata ta koma kamar ta yaro, ke nan ta zama "Mai da tsohuwa yarinya". Baya ga haka ta na karfafa yanayin gudanar jini sannan tana kara kuzarin jiki.




4.  Kara Qibar Jiki.

Aya na taimakawa wajen karawa mutum kiba cikin sauki. Domin samun wannan fa'ida sai a samu aya mai kyau, a daka ta, daga nan sai a zuba ta cikin ruwa ta kwana, idan gari ya waye, sai a  tace a zuba sikari a shanye. Haka za a juri yi. Cikin yardar Allah ramar da mutum ke fama da ita za ta gushe ba da jimawa ba.




5. Inganta Rayuwar Aure.

Ba shakka bincike ya nuna yadda aya ke inganta rayuwar aure. Idan mu ka ce rayuwar aure, mai karatu zai gane inda muka dosa, don haka suma Ma'aurata ana so su waita cin Aya.

Comments