Main menu

Pages

NAZARI DA YUNANIN DA YA KAMATA KIYI AKAN WANDA ZAKI AURA

 



Nazari da tunanin da ya kamata kiyi akan Wanda kika tsayar a matsayin Miji.


- Shin wannan saurayin don Allah kadai kike Kaunarsa, ko kuwa saboda wasu dalilai naki na son duniya? 


- Shin zaki so ace wannan shine Uban 'Ya'yanki?. Kuma shin zakiyi alfahari a Duniya da lahira idan kika haifi da (yaro) mai irin halinsa da yanayinsa?.



- Shin wannan saurayin yana da halaye irin na Tsoron Allah? (Yawan tuna Allah, kiyaye dokokinsa, Bin umurninsa, yin abu don neman yardarsa). 



- Shin wannan saurayin idan ya zama Mijinki zaija ki zuwa ga Aljannah ne, ko kuwa zuwa ga Azabar Allah??. 



- Shin yana Mutunta Mahaifansa da 'Yan uwansa Mata? Idan har yana Mutuntasu to zai mutunta naki. Idan kuma yana wulakantasu to kema sai ya Wulakanta naki. 



- Shin yana yi miki zancen batsa awajen hirarku?  Ko kuma yana Kokarin ta'ba jikinki? (Idan yana da wannan halin to Ki Gujeshi domin shai'dani ne). 



- Shin yaya tarbiyyar gidansu take? Idan gidansu akwai tarbiyyah to zaki ga alamar hakan daga gareshi da kuma Qannensa Mata da Maza. 



- Wajen za'bin saurayi kada Zaqin bakinsa ko kyawun adonsa ya rudeki. Mafiya yawan Samari suna amfani da Zaqin bakinsu ne wajen yaudara da amfani da 'Ya'yan  Mutane. 



Kada ki sa'ba ma Allah don neman yardar Saurayi. Idan kika bama saurayi damar ta'ba jikinki, to lallai Kinci amanar Iyayenki bisa wahalar tarbiyyar da suka baki. 



Kin ci amanar 'Yan uwanki da danginki tunda kin shigo musu da Mummunar Alfasha atsakaninsu. Kin ci amanar Mijin da zaki aura nan gaba.. (Koda shima Mazinacin ne). 



Kin ci amanar Zuriyar da zaki haifa nan gaba. Tunda kika aikata zina kin gurbata Musu jini da wannan dau'dar Zinar taki. 



Mafi girma kuma ita Amanar Allah da kika ci. Domin dukkan gabobin jikinki ya badasu amana ne agareki don kiyi amfani dasu wajen neman yardarSa. 



Manzon Allah (saww) kuwa yace Koda bayan rasuwarsa ana nuna masa ayyukan al'ummarsa. Shin ba zaki ji kunya ba, ace yaga Zina acikin ayyukanki?. 

   Allah sa mudace.

Comments