Main menu

Pages

KI KOYI YADDA AKE HADA TSUMI KALA DABAN DABAN A GIDA

 Manyan Tsumin da suka fi kyau da inganci ga Mace, ga su guda hudu, kinkoyibyadda Zaki hada su.


Tsumin 'ya'yan itatuwa abune me kyau a wajen mace kuma idan kina tareda wannan gida a darusan baya kin karantasu shine naga ya kamata nakawo wasu daga cikin wadanda suka shahara wajen karawa mace ni'ima
(1) Wannan sassaken baure zaki samu ki zuba masa ruwa ki dora akan wuta idan ya tafasa zakiga ruwan ya canja kala saiki sauke sannan ki tace ruwan dama kin daka kanun fari saiki zuba garin sannan ki zuba zuma kadan saiki saka bazar kwaila sannan ki mayar dashi kan wuta idan ya tafasa zakiji yana kamshi saiki saukeshi sannan ki ajiyeshi kina shansa sau2 a rana

(2) Shi kuma wannan da rake akeyinsa wato ki yanka rake kanana kanana kamar alawar yara sai ki saka a tukunya da ruwa ki jefa kanumfari bada yawa ba fa da yar cittar ki itama ba mai yawa ba sannan ki bare dabinon ki cire kwallon ki jefar kwallon saiki dakashi ya zama gari saiki zuba aciki sai ki dora kan wuta ya dahu sosai sai ki sauke ki matse rake ki cire sannan ki tace ruwan sai kuma ki maida kan wuta ki saka mazalkwaila a ciki sai ta narke sai ki sauke kisa a fridge yayi sanyi ki wuni kina shansa

(3) Sai kuma wanda akeyi da kwakwa kawai kisamu aya danya sai dabino ki cire kwallon da danyen zogale da kwakwa da kankana da cukuw sai mazar kwaila ki markadasu ki tace ruwan sannan kidauko nonon rakumi ki zuba ki gauraya ki wuni kinasha zakiga wani ruwa me maiko yana kamshi

(4) Na hudu kuma ganyen zogale Zaki dafa bayan ya dafu saiki tace ruwan kana ki yanyanka cocumber aciki ki zuba aya da farin goro ki markadasu dukkansu saiki tace ruwan sannan ki zuba madara peak ko luna kisha saidai kamar irin wannan yana saka wasu matan gudawa saboda wannan ruwan zogalen amma idan dama kina shan zogale kada kibar wannan hadin.

Comments