Main menu

Pages

AMFANIN COCUMBER GUDA 8 DA BA KOWA YA SANI BA

 



Abu 8 na ban mamaki da Cocumber ke yi a jikin dan adam


Cocumber da a galibin lokuta ake sa shi cikin rukunin kayan Salad, shi ma kayan marmari ne da ke da matuƙar muhimmanci ga jikin dan adam.


Yana ƙunshe da sinadarai masu ƙarfi irinsu, Vitamins da antioxidants da ke taimakawa wajen warkewa da kariya daga cututtuka.


Cocumber na da ƙarancin sinadarin calories, sannan akwai ruwa sosai a jikinsa da sinadarin fiber, hakan ya sa yake da kyau wajen taimaka wa jiki da ruwa da rage ƙiba.


A wannan maƙala za mu zayyana hanyoyi 8 da cin Cocumber zai taimaka wa lafiyarku.


1. Sinadarai masu gina jiki

Cocumber ba shi da sinadarin calories sosai mai sanya ƙiba sai dai yana kunshe da vitamins da minerals masu matuƙar muhimmanci.


Kowane guda wanda ba a fere ba, yana kunshe da wadan nan sindaran:

- Calories

- Carbs

- Protein

- Fiber

- Vitamin C

- Vitamin K

- Magnesium

- Potassium

- Manganese

Ba lallai sai an cinye guda za a samu biyan buƙata ko waɗannan sinadaran ba, ko raba shi aka yi gida uku aka ci kashi ɗaya to za a samu duk waɗan nan sinadarai yadda ake bukata a jikin dan adam.


Sannan Cocumber kusan ruwa ne baki ɗayansa, domin kashi 96 cikin 100 na kayan itacen ruwa ne zalla.

Idan ana son tabbatar da ganin ya yi aiki yadda ake bukata, to kar a fere shi, ya fi amfani idan aka cinye shi har ɓawonsa.

Yana maganin ciwon damuwa da saisaita lafiyar ƙwaƙwalwa


2. Sinadarin Antioxidants

Yana kunshe da sinadarin antioxidants da ke bayar da kariya daga kamuwa da cutuka irinsu kansa da ciwon zuciya da hanji da garkuwa daga wasu cutukan.


cin gurji zalla na bai wa mutanen da shekarunsu suka ja garkuwar da za ta inganta lafiyarsu na tsawon lokaci.


3. Taimakawa jiki ya samu isasshen ruwa

Akwai mutanen da ke da matsalar shan ruwa, wanda hakan ke jawo illa ga lafiyarsu. Sai dai rungumar dabi'ar cin gurji na iya maye wannan gurbin.


Bincike ya nuna cewa kashi 96 cikin 100 na Cocumber ruwa ne zalla, kuma wadanda suka raja'a wajen cin sa shi kaɗai ko ba sa shan ruwa za su kasance cikin wadatacciyar lafiya da kariya daga cutuka.

Sannan yana hana jiki bushewa kana yana gyara fata.


4. Rage ƙiba ko tumbi

Cin Cocumber na taimakawa wajen rage ƙiba ta hanyoyi daban-daban.

Na farko sinadarin calories ɗin da ke ciki babu yawa. Don haka duk cin da za a masa ba ya sa ƙiba.


Don haka ana iya sarrafa shi ta hanyoyi da dama cikin abinci ko lemu ko ruwan sha.

Sannan, yawan ruwan da ke jikinsa na taimakawa wajen rage ƙiba ko tumbi idan ana amfani da shi a kai-a kai.


5. Taimakawa wajen yaƙi da ciwon suga

Bincike da dama sun nuna cewa Cocumber na iya taimakawa wajen taƙaita ciwon suga da kuma wasu ilollinsa ga jikin dan adam.

Yawan cin Cocumber na narkar da suga a cikin jini don haka yawaita cinsa na hana kamuwa da ciwon suga ko diabetes.


6. Inganta narkewar abinci da ba-haya cikin sauƙi

Cin Cocumber na taimakawa ciki da samun bahaya cikin sauki

Rashin samun bahaya ko wahala da cushewar ciki abu ne da ke addabar galibin mutane a wasu lokutan, don haka yawaita cinsa na kawo sauƙi da waraka saboda yawan ruwan da yake kunshe da shi.

Hakazalika sinadarin fiber da ke cikin gurji na taimakawa wajen narkewar abinci.


7. Yana hana kansar hanji da saisaita kitse a cikin jini

Yawan cin Cocumber na hana kamuwa da ciwon daji ko kansar hanji.


Sannan Cocumber na saisaita kitse a cikin jini da hana tsufa ko yamushewar jiki.


8. Ni'ima ga mata da gyaran fata

Gurji na ƙarawa mace ni'ima idan aka markada shi da madara ko yoghourt.


Hakazalika ana iya shafa shi a fuska ko jiki domin yana maganin ƙonewar fata sakamakon zafin rana.

Comments