Main menu

Pages

FALALAR AZUMIN TASU'A DA ASHURA

 


Falalar dake cikin azumtar Tasu'a da Ashura

Azumin ASHURA yanada matukar falala kuma ana yin sane ranar goma ga watan muharram manzon Allah SAW yana azumtar ranar ASHURA Kuma yayi umurni da ayi kamar yadda yazo cikin wani hadisi:-

ﻪﻠﻟﺍ ﻲﺿﺭ ﺱﺎﺒﻋ ﻦﺑﺍ ﻦﻋ

ﻲﻠﺻ ﻪﻠﻟﺍ ﻝﻮﺳﺭ ﻥﺃ ،ﺎﻤﻬﻨﻋ

ﻡﻮﻳ ﻡﺎﺻ :ﻢﻠﺳﻭ ﻪﻴﻠﻋ ﻪﻠﻟﺍ ،ﻪﻣﺎﻴﺼﺑ ﺮﻣﺃﻭ ﺀﺍﺭﻮﺷﺎﻋ

ﻪﻴﻠﻋ ﻖﻔﺘﻣ


FASSARA

Ankarbo hadisi daga ibn Abbas rta hakika manzon ALLAH SAW ya azumci ranar ashura kuma yayi umarni da azumtarsa Buhari da muslimu suka Ruwaito shi

Wannan hadisi yana kara tabbatar mana muhimmancin azumin ASHURA Shima azumin TASU'A bayaninsa yazo cikin wani

hadisi kamar haka:-

ﻪﻠﻟﺍ ﻲﺿﺭ ﺱﺎﺒﻋ ﻦﺑﺍ ﻦﻋ ﻪﻠﻟﺍ ﻝﻮﺳﺭ ﻝﺎﻗ :ﻝﺎﻗ ﺎﻤﻬﻨﻋ

ﻦﺌﻟ : ﻢﻠﺳﻭ ﻪﻴﻠﻋ ﻪﻠﻟﺍ ﻲﻠﺻ

ﻦﻣﻮﺻﻷ ﻞﺑﺎﻗ ﻲﻟﺇ ﺖﻴﻘﺑ

ﻢﻠﺴﻣ ﻩﺍﻭﺭ ،ﻊﺳﺎﺘﻟﺍ ،


FASSARA

An karbo hadisi daga dan Abbas rta yace:- MANZON ALLAH SAW yace:- idan rayuwata tayi saura zuwa shekara mai zuwa zanyi azumin TASU'A Muslimu ya ruwaito shi.

Idan muka dubi wadannan hadissan guda biyu zamuga cewa manzon ALLAH SAW

ya baiwa azumin TASU'A DA ASHURA muhimmanci saboda haka sai muyi kokarin aiwatar dasu gobe da jibi, give Tara ga wata jibi goma ga wata.

ALLAH YABAMU IKON AIWATARWA BISAGA

IKHLASI KUMA YASA MUDACE AMEEN

Comments