Main menu

PagesYadda Ake yin Egg Sauce


INGREDIENTS:

1.Eggs

2.Albasa, attarugu/tattasai

3.Curry, Maggi, salt, garlic and curry powder

4.Oil.


PROCEDURE: Farko zaki jajjaga kayan miyan duka su daku sosai, sai ki zauna ki yanka albasa dinki isasshe ko kuma ki niqa.Daga nan sai ki dauko frying pan ki sa a wuta, ki sa masa mai kamar 3 spoon, sai idan ya fara zafi sai ki juye dukkanin albasan ki, ki soya man dashi, daga nan sai ki juye kayan miyan, kisa maggi, gishiri, curry kadan. Ki cigaba da soya shi, kuma a lura da wuta, saboda ana so ya dan dahu kayan miyan musamman idan dayawa ne, zaki iya dan rufe kayan miyan koda na 2mnt ne saboda yayi taushi in ba ruwa zaki iya diga ruwa.Daga nan sai ki dauko eggs din wanda already kin fasa kin kada sai ki juye, ki jujjuya su hade sosai. Idan kina so yayi dunkule dunkule, zaki barshi ne har sai ya fara soyuwa, sai kina juya shi ba tare da kin barbaza ba. In kuma kina so sai ki barbaza shi. Kwai din na gama soyuwa sai ki sauke kiyi serving.Another method 

Shi kuma wannan wasu suna fasa kwai ne a kwano, sai su juye dakakken kayan miya da albasa din su a cikin kwai din, sai su sa mai ya dan yi zafi sai su juye shi ya soyu. Ana cin egg sauce da Plantain, potatoes, yam, dama sauran su.


Comments