Main menu

Pages

KO KA JANYE KALAMANKA KO MU MAKA KA KOTU, QUNGIYAR MATAN FIM GA NAZIR



 Kunyigar matan kannywood sunyi kira ga sarkin waka ya janye kalamansa ko su kai shi kotu

Kunyigar matan kannywood sunyi kira ga sarkin waka ya janye kalamansa ko su kai shi kotu

Matan kannywood

A yau din nan muka samu rahoton wata takarda ta fito daga shugabancin hauwa A. Bello kan maganganu sarkin waka nazir M Ahmad da yayi ga yan kwana kin nan akan maganar mama ladin cima.



 

Wanda maganganun shi sun tada zaune tsaye a masana’antar kannywood din shine kungiyar matan kannywood association suka fitar da takarda zuwa ga Nazir M Ahmad sarkin waka ga abinda takarda ke cewa.



“Assalamu alaikum,

Kungiyar matan ‘yan kannywood women association of Nigeria (k-wen) karkashin jagorancin shugabancin ni shugabar kungiyar a madadin yan kungiya.



Duba da abin da ya faru wanda Nazir M Ahmad yayi wasu kalamai na chin zarafi ga mata masu sana’ar fim muna kira a gare shi da ya janje kalamansa cikin kwana ukku da yau in kuwa bai yi haka ba zamu kaishi kotun musulunci bisa tuhumar yayi mana kazafi.

Comments