Main menu

Pages

TOFA! WANNAN SHINEA BINDA YA SAMU SADIQ SANI SADIQ

 TOFA! KOTU TA YI UMARNIN  DANKO JARUMI SADIQ  SANI SADIQ KAN ZARGIN ALMONDS HANA


 Alkali Sagir Adamu na wata kotun Musulunci da ke zama a Hotoro masallaci ya bukaci dan sandan kotu ya cafko masa jarumin kannywood Sadiq Sani Sadiq Wani mashiryin fim mai suna Aliyu Adamu Hanas ne ya maka shi a kotun sakamakon karbar kudi har dubu tamanin amma ya ki halartar shirya fim din kuma ya ki biyan sa Kotu ta aike wa jarumin da sammaci amma ba a same sa ba, ta umarci a manna a gidansa kuma ya ki zuwa kotun, lamarin da ya tunzura alkali ya umarci a kama  shi.
 Wata kotu mai zama a jihar Kano ta bai wa dan sandan kotu umarnin cafko mata fitaccen jarumin masana'antar Kannywood, Sadiq Sani Sadiq. READ ALSO Dillalin gidaje ya mutu a dakin Otal bayan shakatawa da matar aure Alkali Sagir Adamu na kotun shari'ar Musulunci mai zama a Hotoro masallaci ne ya bayar da umarnin damke jarumin saboda bijirewa umarnin kotun, Freedom Radio ta ruwaito. Kotu ta yi umarnin damko jarumi Sadiq Sani Sadiq kan zargin almundahana.
Tun farko dai, wani mashiryin fina-finai mai suna Aliyu Adamu Hanas ya kai karar jarumin saboda ya bashi kafin alkalami na kudi domin za su fara aikin shirya wani fim, sai dai jarumin ya ki yin aikin. Bayan nan, Aliyu Adamu Hanas ya yi kokarin karbar kudinsa, amma jarumin ya hana shi, lamarin da ya sa ya gaggauta garzayawa gaban kotu domin neman gumin sa.
Daga nan kotu ta aika wa jarumi Sadiq da sammaci amma sai ba a same shi a gida ba, alkali ya umarci a manna masa takardar sammacin a kofar gidan sa da ke Tudun Yola amma kuma ya ki bayyana a gaban kotun.

Comments