Main menu

Pages

  




KUSKUREN DASUKE BATA GIRKI


   GISHIRI

idan kinsan girkinki ke kadai ce ko bai da yawa kiguji yawan amfani da gishiri domin kuwa muddin kina saka wadataccen maggi to gishiri zai dinga miki yawa



   FRIDGE

duk abinda kikasan zaki barshi ya kwana kiguji saka mishi kwai ko kuma madara musamman idan ba fridge zakisa ba



  KIFI

kilura gurin sarrafa kifi beson jagwalgwale hannu yana saurin bata kifi kidinga kulawa



   KANWA

idan kanwarki bata da kyau kobaki da isasshiya kokuma baki da ita to karkiyi danwake domin kuwa bazae taba yin dandanoba hakanan kada kice zaki yawaita shi



   SPAGHETTI

sphagetti batason spices dayawa hakanan bata son adafa ta da tafassahen nama ko ruwan nama dandanonta beyin dadi sedae kisoya nama kijefa aciki ko kuma kisaka mata kifi hakanan koda wasa karkisakawa sphagetti kitse



   CHIPS

ki kula idan zaki soya chips gishiri kawae ya wadatar karkice zaki saka maggi hakan ba gata bane taste din bekai na gishirin dadi



  MASA

Idan xaki waina wato masa ki kula sosai albasa tana kara dadi amma idan tayiwa waina yawa tana bata taste din karkice zaki kwaba ta da albasa koki markada yana sakawa albasar tajima tana bugan kullin har taste din ya chanja.



  DADDAWA

Ita daddawa tana qarawa abu armashi ba ayin farfesu babu daddawa ki kula koda na kifi ne daddawa itace sirrin farfesu hakanan cikawa farfesu Mai ko manja nasa taste din yakoma wani abu daban



 BLACK TEA

kikula wajen dafa black tea bakowanne irin ganyayyaki ake sakawa ba anfison ganyen yazamanto kala guda sauran kuma kayan kamshine idan bahaka ba zeyi daci ko bauri



  PEPPER MEAT

kikula gurin yin peper meat ko chicken dole sekin dan soya sannan kisake hadeshi idan bahaka ba zeyi karni



   TAFARNUWA

 Ita tafarnuwa anfiso asoyata ne afarkon girki nanne taste din yake dadi amma karkice zaki zubata akarshen girki zaki gagara ci musamman miyar kadi hakanan ba asaka tafarnuwa a alale ko dambu da makamantansu

Comments