Main menu

Pages

DABARUN GIRKI DA YADDA AKE SARRAFA ABINCI

 




 DABARUN GIRKI DA YADDA AKE SARRAFA ABINCI



      CIKA WUTA

Ko kinsan balbala wa girki wuta yana tauyewa abinci dadinsa.

~Idan kinaso ki samu ingantaccen abinci mai cikkaken dandano da gardi, wutar da zaki girki ta zama medium, domin yanxu sai kiga a cikin kakankani lokaci an bankawa abinci wuta nan da nan ya dahu.



~Mutanen da in zasu yi abinci suna wuta baya baya su bashi lokaci, sai kiga an daura sanwar miya tun azahar amma sai yamma likis zaa kada sai kaji kanaci kamar zaka tsinke yatsa, sabanin yanxu komai sharp sharp.



~Ko abu ne da ya dangaci soyawa idan zaki cika wuta karshe zaki tarar ciki bai dahuba.

Don haka sai mu kula.




  ALKUBUS


 1 .Alkama

2 .Fulawa

3 .Yeas

4 .Gishiri da mai


Yadda ake sarrafawa

1. Da farko za a tankade garin alkama da na fulawa a hade su waje guda, sai a zuba yis da sikari da gishiri a kwaba, amma yafi na fanke tauri.

2. A rufe a kai shi rana, idan ya tashi sai a zuba mai kadan a kara buga shi.

3. Sai a dauko gwamgwani a na shafa masa mai ana zubawa a ciki, ko kuma kukkula a leda kamar Alala.

4. Sai a turara shi. Ana ci da miyoyi irin daban daban

 

 


  MIYAR DANYAR KUBEWA


1 .Danyar kubewa gogaggiya

2 . Albasa da attarugu

3 .Naman rago

4 .Tattasai da kanwa

5 Tafarnuwa da citta

 

Yadda ake hadawa

Da farko ki daura ruwa dan kadan a tukunya, sai ki kawo kubewarki da ki ka yayyanka kanana ko ki ka goge ta (gurza ta) ki zuba a ciki ki jefa ‘yar kanwa ki rufe ki bari yadahu har ya tsotse ki ajiye a gefe.

 

Ki wanke albasa ki yanka, ki daura mai akan wuta ki sa albasa da tattasai attarugu da tafarnuwa isasshe da citta, ki sa nama ki sa maggi da ruwa ki rufe.

 

Ki bari har sai naman ya dahu tubus, sai ki kawo wannan kubewa da ki ka dafa a gefe ki hade su ki rufe ki bari a wuta kadan (low heat) na kamar minti biyar sannan sai ki kwashe. 


Wannan wata hanya ce ta sarrafa miyar kubewa irin na ‘yan borno..



Za ki iya ci da sinasir ko biski ko tuwo (na shinkafa, dawa,alkama ,gero, semo ‘yar uwa har da tuwon cous-cous..

 

Abin lura

Dafa kubewa ta wannan sigar yana sa shi ya yi yauki sossai.

Sannan miyar yauki in ki naso tayi yauki kar ki cika kayan miya.

Tafarnuwa na gyara miyar kubewa.

Dafa kubewa daban tare da kanwa yakan sashi ya yi Kore shar a ido.. Ya kuma yi yauki sannan ya dahu cikin sauri.

'Ya'yan kubewa suna sa kubewa yauqi.. Amma wasu basu sonshi kina iya ciresu.

 


TUWAN DAWA



Abubuwan hadawa

1 .Nikeken garin dawa

2 .Kanwa da Ruwa


Yanda ake hadawa

Da farko zaki dora tukunyarki a wuta ki sa ruwa daidai misali

Idan ya tafasa sai ki debo garin dawarki da ki ka tankade kisa ruwa ki dama ki zuba a kan tafasasshen ruwan.

Sai ki sa mucciya ki juya don kar ya yi gudaje. Sai ki kawo ruwan kanwa kadan ki zuba ki barshi yayi ta dahuwa.

Idan yayi sai ki tuka zaki ga har yauki yake yi. Idan kin gama tukawa sai ki rufe ya dan turara, zaki ji yana kamshi sai ki malmala.

A sawa maigida da yara

Zaki iya cin tuwon dawa da irin miyar da ki ke so, amma yafi tafiya da miyar kuka ko danyen kubewa.



  MEAT BALLS AND POTATO SAUCE


1 .Nikakken nama

2 .Albasa Attarugu

3 .Tattasai da dankali

4 .Kayan kamshi

5 .Mai da Tumatir

6 .Maggi star


Yadda ake hadawa

Ki sami nikakken namanki, ki mulmulashi kamar kwallo ,in ki ka mulmula ki ka gama sai ki soya ki ajiye a gefe.

Ki bare dankali ki yayyanka su gida biyu, ta tsakiya za ki raba.

Ki yayyanka albasa ki yi jajjage.

Ki daura mai kadan a kan wuta ki sa albasa ki yi blending tumatiri ko ki jajjaga shima ki zuba.

Ki kawo jajjagen tarugu da tattasai ki zuba ki sa dankali da kayan kanshi da maggi sai ki sa ruwa dai-dai yadda zai dafa dankalin ki rufe Ki bari sai dankalin ya dauko nuna sai ki kawo naman ki zuba ki rufe, har ya karisa nuna. Sannan ki kwashe.

Shima za ki iya ci da taliya, makaroni,cous-cous,bredi,shinkafa,da sauran su.




  LEMON ABARBA DA KWA-kWA


Abubuwan hadawa

1 .Abarba 1

2 .Kwkwa (babbah 1)

3 .Madara ta ruwa (1)

 4 . Sugar ,flavour da kamshi me abarba da kwa kwa

Yadda ake hadawa

Da farko Uwargida za ki wanke abarbanki kuma ki yanka kanana sannan ki zuba a blenda ki markada

Idan ya markadu sai ki tace ki ajiye a gefe

Ki fasa kwakwarki itama ki yanka kanana ki markada blenda

Idan ya yi sai ki tace akan ruwan abarbar

Sai ki zuba madara da suga (idan da bukatar suga din) da abin kamshi

Sai ki juya sosai sai kuma ki zuba kankara ko ki sa a furinji tayi sanyi dan tana bukatar sanyi



YADDA ZAKI ADANA TUMATIR YA SHEKARA🍅🍅🍅🍅🍅🍅



Da farko zaki gyara kayan miyanki dukkan abinda kikeso albasa tumatir tattasa attarubu in kina son tafarnuwa ma zaki iya sawa, sai ki kai markade.

 

~Bayan an markado sai ki juyeshi a abin tatar koko to dama akwai kusa a kafe a bango sai ki maqaleshi a jikin kusar zakiga ruwan kayan miyan yana zubewa zakiga farin ruwane yake zuba baa jijigawa sbd in kika jijiga kayan miyanki zai fita amma hakan idan baki jijigaba sai ruwan tumatir din ya ragu ,to amfanin hakan zaisa ki rage lkcn dahuwa tare da tattalin makamashi,i dan kikaga ruwan ya ragu sosai sai ki juye a tukunya kisa wuta ki barshi yayai ta dahuwaa amma zaki diga mai kadan baifi cokali uku ko biyu ba ya danganta da yawan kayan miyan,to idan ya jima yana dahuwa kuma kina dan jujjuyawa sbd kada ya kama yayi kauri.



~To dama kin wanke kwalaben baman ki sai ki dakko tukunya kinzubasu a ciki ruwan yasha kansu sai kisa gishiri a ruwan daga nan ki barshi ya dan yi minti biyar yana tafasa sai ki dakko kwalbar kizuba kayan miyan ki rufe.



Akwai wata takarda a jikin murfin baman to kada ki cire ki jefar sai ki maidata jikin murfin ki rufe haka zakiyi tayi har kayan miyan ya qare sai ki dakko su ki sake murda murfin kwalbar ki qara rufeshi sai ki maidashi cikin wanan ruwan tafasashe ki barshi yadan tafasa da to duk iskar dake cijin kayan miyan nan zata fita.



To inshaa Allah kayan miyan nan ba abunda zaiyi har tsawon shekara, ki lura bayan kin fitar dashi daga ruwan zafin nan to ki lura da murfin zakiga ya loma ya fada ciki this means kayan miyan yayi ba iska a cikin kwalbar.

Comments